Gwamna Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jiihar Kano ta yi alƙawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin ƙara bada damar inganta ilimin matasa a jihar.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi yayin buɗe taron makon matasa, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin duba a kan matsalolin matasa da kuma lalubo hanyoyin da za a magance su.

Taron wanda ya gudanar a rufaffen ɗakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata a ranar Laraba da ta gabata.

A cewar Gwamna Ganduje, tuni an tura sunayen Kwalejin Horas da Malamai ta Sa’adatu Rimi da kuma Kwalejin Koyar da Aikin Noma ta Audu Bako da ke Danbatta ga Hukumar da ke Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) domin neman sahalewa.

Ya ce ya yi hakan ne domin ƙara bai wa matasa damar su ƙara karatu don inganta rayuwarsu da kuma cigaban jihar Kano baki ɗaya.

Wannan na nuna cewa, idan waɗannan jami’o’i suka tabbata Kano tana da jami’o’i guda 4 kenan mallakin gwamnatin jiha.

By Editor