Zamfara: Makarantun sakandare 75 ne a rufe saboda matsalar tsaro

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa har yanzu akwai makarantun sakandare 75 da suke a rufe sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda.

Hakan ya fito ne ta bakin babban sakataren ma’aikatar ilimi ta jiha Alhaji Kabiru Attahiru cikin saƙon fatan alheri a wani taro na kwanaki biyu a matakin jiha na gidauniyar samar da manufofin ƙasa kan jinsi a fannin ilimi NPGE A jihar Zamfara wanda hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta ƙasa da haɗin gwiwar hukumar UNICEF suka shirya a cibiyar horas da malamai ta Zamfara Gusau ranar Laraba.

A cewarsa, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle tana aiki ba dare ba rana domin buɗe makarantun da abin ya shafa nan ba da jimawa ba.

Ya kuma ƙara da cewa makarantun da abin ya shafa sun mafiya yawansi sakandiren mata ne a jihar.

Idan dai ba a manta ba a watan Satumban 2021 ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da sakandire a jihar nan take sakamakon sace ɗalibai 75 da aka yi a makarantar Government Day Secondary School Ƙaya, a Ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.

Babban sakataren ya bada shawarar cewa akwai buƙatar a shigar da masana a fannin ilimi cikin manufofin ƙasa kan ilimin jinsi domin samun nasarar da ake buƙata.

Shi ma a nashi jawabin mashawarcin hukumar UNICEF na jihar, Dr. Ahmed Hashim ya bayyana manufofin kwamitin wanda ya ƙunshi nazarin abubuwan da aka samu daga taron da ya gabata kan NPGE, aikin cikin gida ta hanyar tabbatarwa, kammala shirin aiwatarwa da kuma ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa na jiha.