Daga CMG HAUSA
Jiya Alhamis ne aka gudanar da taron murnar cika shekaru 60, da kafuwar hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Uganda ta kafar bidiyo.
A yayin taron, mataimakin shugaban ƙungiyar sada zumunci da ƙasashen waje ta ƙasar Sin Jiang Jiang, ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata ƙasar Sin da ƙasashen Afirka su haɗa kansu, wajen ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin gina ababen more rayuwa, da gudanar da ƙirƙire-ƙirƙire ta fuskar harkokin sadarwa, da neman bunƙasuwa ta hanyar kare muhalli, domin neman babban ci gaba.
A nata ɓangaren, jakadar ƙasar Uganda dake ƙasar Sin Oliver Wonekha ta bayyana cewa, shekarar 2022 wata muhimmiyar shekara ce, domin a cikin ta ake cika shekaru 60 da kafuwar hulɗar diflomasiyya a tsakanin ƙasar Uganda da ƙasar Sin, kuma cikin waɗannan shekaru da suka gabata, ana ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin ƙasashen biyu, yayin da aka cimma sakamako da dama.
Tana mai cewa, “Ƙasar Sin ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi zuba jari a ƙasar Uganda, wanda hakan ta taka muhimmiyar rawa a fannin raya tattalin arzikin ƙasar Uganda, shi ya sa, gwamnatin ƙasar take godiya matuƙa dangane da taimakon da ƙasar Sin ta samar mata.
Kazalika ƙasar Sin ta samar da taimakon kuɗi ga wasu muhimman shirye-shiryen raya ƙasar Uganda, kamar na gina tashar samar da wutar lantarki da ƙarfin ruwa ta Karuma, da gina manyan hanyoyin mota tsakanin birnin Entebbe da birnin Kampala da sauransu.
Kuma, bisa bayanin da aka fidda, ya zuwa shekarar 2020, ƙarfin cinikayya a tsakanin ƙasashen biyu, ya zarce dallar Amurka har biliyan 1.
Ƙasar Sin ta kuma ba da gudummawa matuka ga ƙasar Uganda, a fannin gudanar da kwaskwarima, da neman ci gaba, bisa tsarin dandalin tattauna haɗin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC”.
Mai Fassarawa: Maryam Yang
