Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya zargi Ministan Kwadago Chris Ngige da taɓarɓarewar tattaunawa tsakanin malaman da ke yajin aiki da gwamnatin tarayya.
Jega, wanda kuma tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ne ya yi wannan zargin yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Arise, a ranar Talata, 5 ga Oktoba, 2022.
A cewarsa, Ministan ne ke da alhakin yajin aikin da aka kwashe watanni bakwai ana yi, bayan da ya mayar da lamarin ya zama na ƙashin kai.
“Ministan Kwadago ba ya taimakawa al’amura, ya koma rikici tsakaninsa da Ministan Ilimi, a ɗaya ɓangaren kuma tsakaninsa da ƙungiyar ma’aikatan Ilimi,” inji Jega.
Farfesan a fannin kimiyyar siyasa ya ce, maimakon ministan yi aiki tare da ASUU da ma’aikatar ilimi don magance matsalar, sai ya sanya tattaunawar ta kasance mai sarƙaƙiya.
Jega ya yi nuni da matakin da Ngige ya ɗauka na yi wa ƙungiyoyin da ke hamayya da juna rajista: Congress of Academics University and National Association of Medical and Dental Academics a wannan makon a matsayin wasu hanyoyin da Ngige zai kawo cikas wajen magance matsalar yajin aiki a tsarin jami’a.
“Kuma yayin da mutane da yawa ke ƙoƙarin neman hanyar da za a magance wannan lamarin domin ɗalibai su koma makaranta su kuma ASUU su koma bakin aiki, shi Ngige ya shagaltu da kawo ƙalubale, yanzu ya kai maganar gaban kotun masana’antu.
ASUU ta ɗaukaka ƙara. Yanzu a yau ya yi rajistar qungiyoyi biyu da ke ƙoƙarin haramta ƙungiyar ma’aikatan Jami’o’i. Idan har aka ƙyale hakan, ina ganin wannan lamarin na iya haifar da matsaloli da yawa fiye da yadda za a iya magance wannan matsalar ta yajin aiki a jami’o’i,” inji Jega.
