Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murnar cika shekaru 65 da kafuwar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Rasha da Sin.
Cikin wasiƙar ta ranar Asabar, shugaba Xi ya ce tun kafuwar ƙungiyar yau shekaru 65 da suka gabata, tana ta ƙara azama wajen kyautata cuɗanya da ɓangaren Sin.
Ta kuma bayar da muhimmiyar gudummawa wajen inganta fahimtar juna, da abota, da amincewa juna tsakanin al’ummun ƙasashen biyu, da ma kara faɗaɗa ginshikin tattaunawa tsakanin al’ummunsu.
Don haka ya yi fatan ƙungiyar za ta dore da wannan kyakkyawan aiki nata, na haɗa kan al’ummun Sin da Rasha.
A ɗaya hannun, shi ma shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, ya aike da makamancin wannan sako ga ƙungiyar.
Mai Fassarawa: Saminu Alhassan
