2023: INEC ta fara tantace ‘yan jarida

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A matsayin ɓangare na shirye-shiryen zaɓen 2023, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta fara tantance ‘yan jarida da kafafen yaɗa labaran da ke da sha’awar yin aiki da ita yayin zaɓen.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet, inda ta ce za ta gudanar da tancewar ce ta intanet kaɗai.

INEC ta ce za ta buɗe shafin yin rijistar ne daga ranar Alhamis, 5 ga Janairu zuwa Lahadi, 5 ga Fabrairu na 2023.

Ta ƙara da cewa, kafafen yaɗa labaran da ke da sha’awar tura wakilansu yayin zaɓen, suna iya shigar da bayanansu ta: via:https://imap.inecnigeria.org

Ta ce ba za ta lamunci shigar da bayanai a makare ba, saboda shafin yin rijistar zai rufe kansa da zarar wa’adin da aka shata masa ya ƙare.

INEC ta ce masu neman ƙarin bayani game da shirin na iya tuntuɓar waɗannan lambobin wayar: 08033141836, 08033802792 da kuma 08032861058.

By Editor