Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar.
A wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na Masarautar Bauchi, Babangida Hassan Jahun ya fitar a ranar Alhamis, ya sanar da cewa Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya naɗa Alhaji Muhammadu Uba Ahmad Kari a matsayin sabon Wazirin Bauchi.
Kan wannan matakin, Uba Ahmed Kari ya maye gurbin Muhammadu Bello Kirfi da aka samu da rashin biyayya wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad.
Wani yanki na sanarwa na cewa: “Majalisar Mai Martaba Sarkin Bauchi tana farin cikin gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki zuwa wajen naɗin sarautar Wazirin Bauchi Alhaji Mohammadu Uba Ahmad Kari ranar Juma’a 6 ga watan Janairun 2023 da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi.”
Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Jihar Bauchi da Masarautar Bauchi sun warware rawanin Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, bisa zargin rashin mutunta Gwamnan Jihar, Bala Abdulkadir Muhammad.
A wata takarda da Sakataren Masarautar, Alhaji Shehu Mudi, ya sa wa hannu, mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Janairu, 2023, an bayyana cewa tsige Bello Kirfi ya biyo bayan matsayar da Majalisar Masarautar Bauchi ta cimma ne.
Babu tartibin dalili a bayyane da ya sanya aka tuve alkyabbar Wazirancin Bauchi daga jikin Alhaji Muhammad Bello Kirfi, illa wata takarda da take da nasabar hakan wacce sakataren majalisar masarautar Bauchi, Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya rattaɓa hannu da laƙabin “Rashin biyayya da ladabi” wa Gwamna Bala Mohammed.
Wasiƙar ta tunɓuke Muhammad Bello Kirfi a matsayin sa na mashahurin mamba na majalisar masarautar Bauchi mai kwanan wata 3 ga watan Janairu na wannan shekara ta 2023, wacce kuma Sakataren Majalisar ya rattaɓa hannu, wani sashin ta yana cewa: “An umarce ni da na hankaltu da takardar da ta fito daga Ma’aikatar Lura da Lamuran Ƙananan Hukumomi mai ba’asin lamba MLG/LG/S/72/T’ ta ranar 30 ga watan Disamba, 2022.
“Bayani da waccan takarda ta ƙunsa shi ne ta zayyana rashin biyayya da ladabin ka wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da kuma Gwamnatin Jihar Bauchi. Takardar ta yi umarnin a dakatar da kai nan take. Dangane da haka, a yanzu an cire ka daga sarautar Wazirin Bauchi da kuma mamba na majalisar masarautar Bauchi.”
A cikin wasiƙar, Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya yi wa tuvavven Wazirin Bauchi fatar alheri a dukkan inda lamuran sa suka dosa nan gaba.
Tuvabben Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammad Bello Kirfi dai, wanda makon da ya gabata ne ya cika shekarun haihuwa 92 a duniya, tantibin abinda ya sanya aka tuve masa rawanin wazirci bai bayyana a fili ba, amma ana kyautata zaton kwakyarar ba ta rasa nasaba da saɓanin siyasa da ke tsakanin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da ɗan takarar neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da ake hasashen Muhammad Bello Kifi ya tsunduma ciki.
Haka zalika, wata kwamishiniya da ke jagorancin Ma’aikatar Bunƙasa Cigaban Ƙanana da Matsaƙaitan Masana’antu na Jihar Bauchi, a ranar Laraba ce ta ajiye aikinta, ta hanyar rubuta wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed wasiƙa da niyyar cewa ta ajiye kujerar ta nan take.
A cikin wasiƙar da ta rubuta wa gwamnan jihar ta hannun sakataren gwamnatin jiha, Barista Ibrahim Kassim Mohammed, ta ce “Maigirma Gwamna, Ina mai matuqar kuzarin gabatar da takardata ta barin aiki, a matsayina na mamba a majalisar zartarwa ta jiha, kuma kwamishina a ma’aikatar gama kai da bunƙasa cigaban ƙanana da matsakaitan masana’antu.
Kwamishinar mai ajiye aiki, Sa’adatu Muhammad Bello Kirfi ba ta zayyana wani dalili ban a barin ajiye kujerar ta nan take, sai ta yi godiya wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed bisa damar da ya ba ta na yin aiki a ƙarƙashin gwamnatinsa.
Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi dai ta aijiye aiki ne jim kaɗan bayan da aka warware rawanin mahaifin ta, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi na Wazirancin Masarautar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu a safiyar ta Laraba.
Har ila yau, a cikin rakacaniyar guje wa gwamnatin ta jihar Bauchi, akwai babban mataimaki (SSA) wa gwamnan jiha akan lamuran ma’aikatar lura da ƙananan hukumomi, Honarabul Harsanu Yunusa Guyava, wanda shi ma ya tiƙar da kujerar tasa, biyo bayan sauke Muhammad Bello Kirfi daga Waziranci a Masarautar Bauchi.
Guyava dai sun fito gari ɗaya ne da tuvabben Wazirin Bauchi, ta yiwu ma akwai dangantaka a tsakanin su.
SSA Harsanu Guyava ya ce: “Tare da ɗimbin godiya wa Allah Mahalicci, haɗi badaɗantaka wa Maigirma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Ƙauran Bauchi) nake son gabatar da takarda ta ta barin aiki a matsayin SSA kan Ma’aikatar Lura da Lamuran Ƙananan Hukumomi ta Jihar Bauchi, daga yau Talata 3 ga watan Janairu, 2023.”
Idan za a iya tunawa dai, Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya dakatar da Wazirin Bauchi, Mohammad Bello Kirfi a lokacin gwamnatin da ta shuɗe a shekara ta 2017.
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed bayan kama ragamar mulkinsa a shekata ta 2019 ya yi sanadiyyar dawo da Alhaji Muhammad Bello Kirfi kan muƙamin san a Wazircin Masarautar Bauchi a ranar 5 ga Agusta, 2022.
