Bayyana kadara: Kotu ta haramta wa DSS tsare shugaban INEC

Spread the love

Daga WAKILINMU

Babbar Kotun Tarayya a Abuja
ta dakatar da karar da aka shigar gabanta na neman tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya dangane da kadarorinsa.

Alƙalin Kotun, M. A. Hassan, ya ce bayanan gaskiya Yakubu ya bayar dangane da kadarorin da ya mallaka kuma daidai da doka, don haka ya ƙi amincewa da ƙarar da aka shigar kan shugaban na INEC.

A zaman kotun na ranar Laraba, alƙalin ya hana hukumar DSS da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) kama Yakubun.

Ya yanke hukuncin ne bayan ƙarar da wani mai suna Somadina Uzoabaka ya shigar da Yakubu da kuma Babban Lauyan Kasa, yana neman Shugaban INEC ya ajiye muƙaminsa ya koma gefe har zuwa lokacin da za a kammala binciken tuhume-tuhumen da ke kansa.

Mai ƙaran ya kuma buƙaci kotu ta haramta wa Yakubu riƙe kowane irin muƙamin gwamnati na tsawon shekara 10.

Da yake maida martani kan ƙarar, Farfesa Yakubu, ya gabatar wa kotun cikakkun bayanai da hujjojin da suka tabbatar wa kotun hanyoyin samun kuɗinsa halastattu ne.

By Editor