Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar.
Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Masarautar ta fitar ranar Alhamis ta hannun jami’in labaranta, Babangida Hassan Jahun.
Sanarwar ta ce za a yi wa sabon Wazirin Bauchin naɗi ne a ranar Juma’a, 6 ga watan da ake ciki a Fadar Masarautar Bauchi.
Wannan na zuwa ne bayan da masarautar ta tuɓe Muhammadu Bello Kirfi a matsayin wazirinta saboda rashin da’a ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.
