Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Majalisar Jama’atu Nasril Islam, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah-wadai da kisan makiyaya 47 da sojojin saman Nijeriya suka yi a Jihar Nasarawa bisa kuskure, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bincike waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban kuliya.
Ƙungiyar ta JNI ta bakin babban sakatarenta, Dakta Khalid Abubakar-Aliyu, a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar Alhamis, ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa saboda asarar rayukan ’yan uwansu da suka yi a yayin harin.
A cewar ƙungiyar, ya kamata gwamnati ta yi bincike sosai kan al’amuran da suka kai ga kisan gilla da aka yi a Doma, inda ta ƙara da cewa kamata ya yi gwamnati ta binciki sojojinta, musamman rundunar sojojin saman Nijeriya a kan lamarin.
JNI ta yi gargaɗin a kan gwamnati ta share al’amarin, inda ta ce, lamarin ya yi muni matuqa, domin an ƙididdige harin da zai haifar da fargaba tsakanin manoma da makiyaya a jihar Nasarawa.
Ƙungiyar Sultan ta bayyana cewa, ’yan Nijeriya na matuqar fatan ganin an ɗauki ƙwararan matakai kan lamarin, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati ta gano mutanen da aka kashe da kuma wuraren da ake kai hare-hare ta hanyar jajanta wa jama’a.
“Aiwatar da ziyarar zai kasance da matuƙar muhimmanci, don hana ramuwar gayya. A bayyane yake, mutane sun fusata saboda yawancin abubuwan da suka faru na baya-bayan nan da sun shafi mutanen da ba su da wata kariya kuma suna buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa.
“Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta biya diyya ga iyalan waɗanda suka rasu, domin yin adalci da kuma hana duk wani abu na ɗaukar fansa ko ramuwar gayya.
“Ku gurfanar da jami’an da aka samu da laifi domin a sauke nauyin da aka ɗora musu, domin su zama misali ga sauran jami’ai.
“Haɗa kai da hukumomin tsaro da abin ya shafa tare da ƙayyadaddun lokaci don kawo aarshen lamarin, aƙalla kau da duk wata barazanar tsaro da ke addabar ƙasar da kuma lalata ƙananan makamai a hannun masu laifi, wanda idan ba a haka ba Nijeriya za ta cigaba, don ganin yadda ake samun ƙaruwar makamai don kare kai a tsakanin ’yan ƙasa, tunda ga dukkan alamu gwamnati ba ta da niyyar yin hakan,” inji ƙungiyar.
