Kada ka ɓata dangantaka saboda siyasa – Nasihar Sarkin Musulmi ga Atiku

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ake tsaka da zazzzafan yaƙin neman zaɓe don tunkarar kakar zaɓe mai zuwa ta 25 ga Fabrairu, Sarkin Musulmi na Sokoto, Mai alfarma  Sa’ad Abubakar (III), ya gargaɗi ‘yan siyasa a kan su kauce wa siyasar zagi da cin mutuncin juna.

 Sultan ɗin ya yi wannan kira ne a ranar Talatar da ta gabata a lokacin amsar baquncin ɗan takarar shugaban ƙasar nan a qarqashin jamiyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya kawo masa ziyara a yayin shirin fara gangamin yaqin neman zabensa a jihar. 

A cewar Sarkin Musulmi: “Duk abinda mutum zai yi, ya ji tsoron Allah, idan har ka yarda Allah ne yake bayarwa kuma yake hanawa, za ka yi nasara kuma ka yi kyakkyawan ƙarshe a rayuwar nan. Wannan rayuwar zama ne na wucin-gadi. Dole ne mu yi aikin don gyara lahira” inji shi. 

Ya ƙara da cewa, don tabbatar da waɗancan kyawawan halaye, kada ka sake ka zagi mutane. Kuma kada mu ɓata alaƙa da abota saboda banbancin jam’iyya. Domin a cewar sa, Allah yana ba da mulki ga wanda ya so, kuma yana ƙwace shi a duk lokacin da ya ga dama.

Daga ƙarshe Sarkin musuluncin ya bayyana cewa, dukkan ɗaukacin ‘yan Nijeriya da suke a mabanbantan jam’iyyu ya kamata su kasance masu gaskiya da riƙon amana. Sannan kuma su kasance suna yin hakan a cikin gaskiya da tsarkin zuciya. Ma’ana dai, a ji tsoron Allah kawai.

By Editor