Ba duk finafinan Nollywood ne ake iya hasashen ƙarshensu ba – Tana Adelana

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Jaruma a masana’artar finafinai ta Kudu, Tana Adelana ta musanta faɗar mutane da suke cewa, dukka finafinan da masana’antar Nollywood ke fitarwa mai kallo zai iya hasashen yadda zaren labarin zai ci gaba har ya zuwa ƙarshe. 

Jarumar ta mayar da martani da cewa, ba fa kowanne fim daga cikin finafinan Nollywood ne mai kallo zai iya hasashen yadda labarin zai ci gaba, domin akwai waɗanda sai dai mai karatu ya tsumayi zuwan ci gaba, wanda zai zo masa a ba yadda ya yi tunanin sa ba.

A cikin tattaunawar ta a shirin Saturday Beats, jaruma Tana, ta ce, “ba wai na ce dukka finafinan Nollywood ba a iya hasashen su ba, kuma ban ce dukka na ɗauke da karsashi ko zaƙuwar mai kallo na muradin ganin ya kai ƙarahe ba, sai dai hakan ba yana nufin dukka ba su ɗauke da waɗannan ba.

Kamar dai yadda finafinan Hollywood suke, waɗanda ni ma Ina kallon su, ba kowanne fim ne za ka tarar ya zo wa mai kallo a ba-zata ba, akwai finafinai da dama da suke da saurin ganewa, ko aka yi su da sauqi, haka ma anan Nollywood.

Akwai finafinai da yawa da ba za a iya hasashen yadda suke tafiya ba. Abinda kawai za ka yi ka tabbatar shi ne, ka nemi kafafen da ake sanya shahararrun finafinan Nollywood, wanda shahararrun jarumai suka yi.”

Dangane da tsaurin da aka fi haskata da shi a mafi yawa na finafinan da ta ke fitowa, jarumar ta ce, “a wasu lokutan zan iya cewa a zahiri ma Ina da tsauri, domin mutum ce ni mai dokoki tare da kafiya akan abinda na yarda da shi.”

Daga ƙarshe, jaruma Tana Adelana ta amsa tambaya kan yadda ta ke kula da jikinta ta yadda a kodayaushe ta ke sheqi, jarumar cewa ta yi, “Ina cin abindan da ya dace, Ina yawan shan ruwa masu yawa, sannan Ina iya ƙoƙari na gujewa kemikal (chemicals).”

By Editor