Daga AISHA ASAS
Biyo bayan mutuwar mawaƙi Mohbad mai shekaru 27 da haihuwa, mutuwar da ta taɓa mutane da dama, wanda ta sa aka tada ƙura, da ta yi sanadin samun shahara ga mawaƙin fiye da lokacin da yake raye.
Mutuwar wadda take ɗauke da ruɗani da neman sanin ababe da dama dangane da silar mituwar matashin mawaƙin. Da yawa sun zargi ubangidan mawaƙin, wato fitaccen mawaƙi Naira Marley, wanda aka ruwaito cewa, mawaƙi Mohbad ya jima yana kai kuken cin zafarin da yake masa a matsayin sa na ubangidansa, wanda har a wasu waƙoƙinsa yana ƙoƙarin bayyana halin da yake ciki, wanda da yawa mutane sai bayan mutuwar tasa ne suka fahimci kururuwar neman taimako da yake yi a waƙoƙin.
Raɗe-raɗin sun nuna cewa, mawaƙin wanda ya yi yunƙurin rabuwa da ubangidanshi mawaƙi Naira Marley, da suke cewa shi ne silar da ya sanya masa guba ya kashe shi, wasu kuwa sun ce an haɗa kai da likitocin don sheƙe mawaƙin.
A wani ɓangare kuwa mahaifin mawaƙin na ɗaya daga cikin waɗanda aka tuhuma kan mutuwar ɗan nasa, inda a wata majiya ta ce, an ba wa mahaifin nasa tushiyar baki daga waɗanda suka yi sanadin mutuwar mawaƙin, inda suka nemi shirunsa tare da musanta wasu ne suka kashe ɗansa, ma’ana ya ayyana mutuwar ɗan nasa da mutuwar Allah, tare kuma da gaggauta kai shi makwancinsa, don gudun allura ta tono galma.
A wata ruwaya mahaifin na da hannu a mutuwar mawaƙin, inda ake zargin yana jin haushinsa sakamakon yadda yake ba wa mahaifiyarshi kulawa wadda ba ya yi mashi, hakan ya kai shi da fushin zuciaya da ya yi ajalin ɗan nasa.
A ɓangare na ƙarshe, matar mawaƙin ta shiga layin waɗanda ake zargin kashe mawaƙin, inda aka bayyanata a matsayin mace marar halin ƙwarai. Da yawa sun shede ta da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi, baya ga haka ta kasance mai hulɗa da wasu mazan baya ga mijinta, ciki kuwa har da ubangidan nasa, wato Naira Marley, wanda ake zargin sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin ganin mawaƙi Mohbad ya bar duniya.
Da wannan ne hankali ya raja’a kan rayuwarsa da matar tasa, har suka tsaya cak kan kallon jinjirin ɗansa mai kimanin watanni biyar da haihuwa, inda suka gano babu wata alama a jikin yaron da zata nuna mawaƙi Mohbad ne ya yi sanadin zuwansa duniya.
Da wannan dandazon ‘yan Nijeriya suka nemi matar da ta je asibit don a gudanar da gwajin ƙwayoyin halitta, don samun tabbacin wanda ya yi cikin sa. Ta wannan hanyar ce kawai za a iya amsa tambayar ko mawaƙi Mohbad ne ya yi mata cikin, ko kuwa ɗaya daga cikin mazajen da ta ke tarayya da su.
Da yawa sun yi amana da wannan kira da aka yi ga matar mawaƙin, wanda suke ganin hanaya ce da za ta iya warware har binciken wanda ya kashe mawaƙin.
A cikin haka ne, aka samu wasu tsiraru da suka yi Allah wadai da wannan kira da ɗinbin mutane suka yi ga matar.
Jaruma Anita Joseph ta bi layin waɗanda ke ganin hukuncin a matsayin cin zafari, kasancewar matar a yanzu tana cikin takaba.
Jarumar ta yi tir da mutanen da suka yi wannan kira ga matar, alhali tana cikin baƙin cikin rasa mijinta, wanda ta ke ganin hakan a matsayin rashin dacewa, da kuma rashin tunani.
Furucin na jarumar ya harzuƙa mutane da dama, ganin ta faɗi cewa, ba hurumin ‘yan Nijeriya ba ne su ne mi wannan gwajin ba, duba da cewa matar tasa mai suna Omowunmi tana cikin tashin hankali na rasa miji da ta yi. Wannan na nufin tana goyon bayan matar ne, wanda hakan ya harzuƙa jama’a da har ya kai ana jifarta da kalamai masu zafi.
A cikin mutanen da ke mayar da martani ga jarumar, ɗaya daga ciki ya yi martani mai zafi da ya harzuƙa jarumar inda ita ma ta mayar masa da takwaran irin tasa.
Ya ce, “ga dukkan alamu dai kina hauka ne, ‘yar manuniya dai ta nuna wannan yaron ba na Mohbad ne ba, don ba ta inda kamaninsa da yaron take, don haka ni banga laifin neman matar ta yi gwaji don a tabbatar ba, ita ma babu dalilin da zai sa ta tsorata da gwajin matuƙar dai tana da gaskiya.”
Ita kuwa jaruma Anita ta mayar masa da martani ta hanyar zagin tsohuwar da ta haife shi.
