‘Yan Majalisar Wakilai sun mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da ake yi game da batun saya musu motocin alfarma

Spread the love

Majalisar Wakilai ta ƙasa ta mayar da martani a kan ce-ce-ku-cen da ‘yan ƙasa ke yi game da batun saya wa mambobinta su 360 sabbin motocin alfarma.

A cewar Majalisar, za a sayi motocin ne don aikin ofis, kuma kuɗin da ake cewa za a sayo motocin bai kai yadda ake zuzutawa ba.

A hirarsu da BBC, Honorabul Kabiru Alasan Rurum mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya daga jihar Kano a Majalisar, ya ce:

“Tun da mu ne karkatacciyar bishiya mai daɗin hawa kusan duk abubuwan a kanmu yake, ya kamata idan za a yi abu a yi shi ga baki ɗaya, ma’ana a kasafin kuɗin bana nawa aka ware na saya wa ofishin shugaban ƙasa motoci, da mataimakinsa da kuma ministoci haka a dukkan mataki har a zo kanmu.”

Ya ƙara da cewa, ”Idan har aka yi la’akari da ba mu kaɗai za a saya wa motocin ba, to shi ne aka yi mana adalci, amma saboda mu ne aka zaɓa shi ne aka yi laifi.”

Ɗan Majalisar ya ce su kansu sun damu da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, kuma kowa a cikinsu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya taimaka a wannan gaɓar don a samu sauƙi.

Wannan taƙaddama dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, ya amince wa majalisar wakilan ƙasar kashe naira biliyan 70 daga cikin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin 2022, batun da ya janyo ƙorafe-ƙorafe daga wajen ‘yan ƙasar saboda matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

Ƙungiyoyin kare fararen hula na daga cikin ƙungiyoyin da suka fara ƙorafin inda suka ce matakin majalisar na sayo waɗannan motoci ga ‘yan majalisar ƙasar a daidai lokacin da talakawa ke fama da matsin rayuwa ba komai ba ne illa rashin damuwa da halin da ake ciki.

By Editor