Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta ƙaddamar da tubabbun ‘yan daba 50 waɗanda ta ɗauka aikin ɗan sanda a jihar bayan kammala horo na wata biyu.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa, ta ce an zaɓo mutanen ne daga ƙananan hukumomin Municipal, da Dala, da Ungoggo, da Gwale, da Fagge, inda aka ɗauki mutum 10 kowaccensu.
Da yake jawabi ranar Litinin a birnin Kano, Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ya ce ‘yan daba 222 ne suka tuba tare da miƙa makamansu a birnin.
Birnin Kano ya fuskanci hauhawar faɗan daba da kuma ƙwacen waya daga matasa masu ɗauke da makamai musamman a watannin tsakiyar 2023, a cewar ‘yan sanda.
“Wannan salo umarni ne na Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu da ya bai wa dukkan rundunonin ‘yan sanda cewa su duƙufa wajen aiwatar da tsaro tare da al’umma,” inji kwamishinan.
