Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi (SAW). Cikin yardar Allah, a kwana a tashi, mai girma Kwamishinan Addinai na Jihar Kano, ya kusa cika kwana 100 da shiga ofishinsa mai albarka.
Domin mai girma Kwamishina Hon Sani Auwalu Ahmed Tijjani ya shiga ofis ne a ranar 3 ga Agusta, 2023, bisa sahalewar Mai Girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Cikin waɗannan kwanaki da mai girma Kwamishina ya yi a ofis, an gudanar da muhimman ayyuka da suka shafi haɗin kai na musulmi, musamman ƙoƙari da yake yi wajan ganin an samu cikakken haɗin kai tsakanin malamai, musamman idan an samu saɓanin fahimta, a warware saɓanin cikin ilimi da dattaku, ba tare da an ci mutuncin juna ba.
Rubutun zai yi saƙo sosai a ce za a zayyano nasarorin da aka samu a rubutu ɗaya, sai dai za mu raba saƙon zuwa gida biyu ko uku.
Ziyarce-ziyarcen Kwamishina:
Mai girma Kwanishinan Addinai na Jihar Kano bayan da ya shiga ofis, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauki himmar kai ziyara gidajen manyan malamai na jihar kano.
Duk wani sashi na ƙungiyar addinin musulunci, Kwamishina ya kai ziyara, inda aka tattauna muhimman batutuwa, musamman neman haɗin kansu wajan ganin an daƙile saɓani da ake samu a tsakanin malamai.
Mai girma Kwamishina ya bayyana saɓanin malamai da ake samu, wanda yake haifar cacar baki mara ma’ana, inda daga ƙarshe abun yake kaiwa ga jami’an tsaro a matsayin babban abun takaici.
Ƙarƙashin haka Hon. Kwamishina ya ce, insha Allah za a kafa majalisar shura, wadda aikinta shi ne tsawatarwa ga duk wani malami da ake ganin yana karantarwa da salon da bai dace ba, idan kuma an samu saɓani, su waɗannan majalisa na shura, su ne za su ɗauki ragamar gayyatar waɗannan malamai ta tattauna da su tare da tattaunawa da su ba wai jami’an tsaro ba.
Kashi na ɗaya cikin wannan rubutu zai tsaya nan, kashi na biyu yana tafe insha Allah.
Aminu Ɗan Almajiri shi ne
S.A MEDIA ga Kwamishinan Harkokin Addinai, Jihar Kano
