Yadda bikin auren jaruma Rashida Maisa’a ya gudana

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

A ranar Asabar ɗin da ta gabata, 11 ga Nuwamba, 2023 ne aka ɗaura auren jaruma a Kannywood Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a, da angonta Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan Matasan Gwoza.

An ɗaura dai a layin Malam Bello a Unguwar Daurawa, daura da babban Titin Maiduguri a cikin garin Kano, kuma an samu halartar jama’a masu yawa da suka shaida an ɗaura auren.

Ita dai Rashida Adamu Abdullahi ba ta shirya wani taron shagulgulan biki ba, kamar yadda jaruman fim suka saba yi. An dai tara malamai a gidanta inda suka wuni suna karatun Alƙur’ani mai tsarki, sa’annan da yamma an ɗan yi taron biki a ƙofar gidan inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarci wajen domin taya ta murna.

‘Yan fim dai da dama sun halarci wajen taron bikin domin taya ta murna.

A cikin wani saƙon godiya da ta wallafa a shafin ta na Facebook, amarya Rashida Adamu Abdullahi, ta yi godiya ga dukkan jama’ar da suka halarci taron ɗaurin auren nata da ma waɗanda suka aika mata da saƙo na taya ta murna.

Daga cikin jaruman da suka samu halartar taron bikin na daga ‘yan’uwanta kuma abokanen sana’arta mata akwai Hadiza Kabara, Hadiza Saima, jaruma Rahma, da sauransu.

Da fatan Allah ya bada zaman lafiya da ƙaruwar arziki.

By Editor