Daga BASHIR ISAH
Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya bai wa ‘yan ƙasa tabbacin cewa ba da daɗewa ba za a bayyana sakamakon binciken da suke gudanarwa game da harin kuskuren da sojoji suka kai ƙauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna kwanan nan.
Sama da mutum 100 ne suka mutu sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin bayan da jirgin sojiji mara matuƙi ya jefa wa masu maulidi bom har sau biyu a Tudun Biri.
Domin gano haƙiƙanin abin da ya faru hakan ya sa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin a gudanar da bincike kan bala’in.
Janar Musa ya ce, “Tabbas za a bayyana sakamakon binciken bayan kammalawa ga al’umma.
“Gwamnatin Tarayya na kula da lamarin, tana aiki a kai, kuma ina da tabbacin ba da daɗewa ba za a bayyana wa duniya sakamakon binciken.”
Janar ɗin ya bayyana haka ne a wani shirin da tashar Channels Television da ta yi da shi a ranar Talata.
Kazalika, ya ce tabbas duk wanda aka gano da hannu cikin wannan iftila’in zai fuskanci hukunci.
