Kasafin 2024: Ba a ware wa ƙidayar 2024 ko sisi ba, inji Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

’Yan kwamitin Majalisar Dattawa kan kasafin kuɗi sun kaɗu a ranar Talata bayan da aka sanar da su cewa babu wani tanadi da aka tsara na ƙidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2024 a cikin ƙudirin kasafin kuɗin hukumar ƙidaya ta ƙasa.

Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da yawan al’umma ta ƙasa Sanata Abdul Ningi (PDP Bauchi ta tsakiya) ne ya sanar da ’yan majalisar halin da ake ciki a lokacin da yake gabatar da rahoton kasafin kuɗin NPC na 2024 ga kwamitin tattara bayanai.

Ya shaida wa kwamitin cewa idan ba a samar da kuɗin ƙidayar a cikin kasafin kuɗin ƙasar ba, ƙasar za ta yi asarar kusan Naira Biliyan 200 da hukumar ƙidaya ta ƙasa ta kashe.

Sai dai ya bayyana wa kwamitin cewa NPC za ta bayyana ranar Laraba tare da bayanan nawa suke buqata don gudanar da ƙidayar jama’a a shekarar 2024.

By Editor