Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, NSCDC, ta ce ta bayar da lasisin gudanar da aiki ga kamfanoni masu zaman kansu 93, PGCs, a shekarar 2023 domin karfafa tsaron kasa.
Kwamandan hukumar ta NSCDC Janar Ahmed Audi ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai a hedikwatar hukumar ranar Laraba a Abuja.
Audi ya ce daga cikin jimillar PGC 1,412 da hukumar ta yi wa rajista, 92 an rufe su a fadin kasar nan saboda wasu laifukan da suka sava wa aiki amma 24 daga cikin PGC da suka kasa cika a shekarar da ta gabata an rufe su.
“Bayan an rufe su, an umarce su da su bi tare da gyara dalilan da aka sanya musu takunkumi, kuma bayan sun cika wasu sharudda da doka ta gindaya, mun amshe 24,” in ji shi.
Ya kara da cewa bayar da lasisi, sa ido, horarwa, da kuma lura da ayyukan PGC na daya daga cikin manyan hukunce-hukuncen da hukumar ta NSCDC ta samu ta samar wa kanta wata hanya ta wannan fanni.
A cewarsa, PGCs sun sami damar cimma burin da ake zato wajen ganin sun inganta ayyukan tsaro saboda yaduwa a cikin lunguna da sako na kasar nan; don haka irin yadda jami’an tsaro ke amfani da su wajen tattara bayanan sirri na asali.
“Mun samu ci gaba sosai saboda sun taimaka sosai kuma muna samun bayanan tsaro masu amfani daga gare su, wanda ya taimaka mana wajen tabbatar da tsaron kasar,” in ji shi.
