Kisan Filato: Shettima ya ziyarci al’ummar Bokos, ya ba da tabbacin yin adalci ga waɗanda abin ya shafa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai wadanda hare-haren wuce gona da iri da aka kai kan al’ummar kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos na Jihar Filato su samu adalci kuma mazauna yankin sun tsira.

Mataimakin Shugaban Kasar, Kashim Shettima, ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci al’ummomin da rikicin ya rutsa da su a jihar Filato domin jajantawa jama’a da gwamnatin jihar kan kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.

Da yake shan alwashin cewa dole ne a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Filato da sauran sassan kasar nan. “Muna matuqar jajenta muku bisa abin da ya auku sannan muka yi muku albishir cewa gwamnati ba za ta haqura ba sai an kamo wadanda suka aikata wannan mummunar abu.

“Lallai gwammati ba za ta yi kasa a guiwa ba sai mun ga bayan wadannan mutane da ba su kaunar zaman lafiya a kasar nan,” inji Shettima.

Idan ba a manta ba Manhaja ta buga labarin yadda mahara suka yi wa wasu masu bikin Kirsimeti, kisan kare dangi, inda suka kashe sama da mutum 100, suka babbake gidaje da motoci sannan suka arce cikin daji.

By Editor