Ga duk mai bibiyar kafafen yada labarai zai ji cewa, Nijeriya ta kara shiga tsaka mai wuya kan yawan bashin da kasar ke kara ciwo wa kanta.
Yawan bashin da gwamnatin Nijeriya ta ciyo ya karu zuwa Naira tiriliyan 42, a cewar Ofishin Kula Basuka na Kasa (DMO).
Ofishin ya cewa a cikin wata uku, daga Maris zuwa Yuni na 2023, Nijeriya ta ciyo karin bashin Dala biliyan uku, wanda ya sa abin da ake bin ta karuwa zuwa Dala biliyan 103.31 daga Dala biliyan 100.
Hakan na nufin idan aka raba wa ’yan Nijeriya mutum miliyan 200 bashin, kowannensu zai biya Naira 210,000.
Idan aka kwatanta da kasafin Naira tiriliyan 27.97 na shekarar 2024 da Shugaba Tinubu ya gabatar a watan Disamba, bashin ya ninka kasafin sau biyu da doriya.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce, “basukan da ake bin mu sun karu me saboda rancen da Gwamnatin Tarayya ta karba domin cike gibin da aka samu a kasafin 2023 da kuma basukan da gwamnatocin jihohi da Birnin Tarayya suka ciyo,” a cikin wata ukun.
DMO ya bayyana cewa, a tsawon watan ukun basukan cikin sun karu zuwa Naira tiriliyan N27.23 (Dala biliyan 63.24); amma ba a samu kari na kasashen waje ba daga Naira tiriliyan 16.61 (Dala biliyan 39.96).
A karshen watan Maris na 2023, Naira tiriliyan 24.98 (Dala biliyan 60.1 ne bashin da ake bin gwamnatocin a cikin gida.
DMO ta bayyana cewa fiye da rabin basukan da gwamnatocin suka ciyo an karve su ne ta hanyar jingina ko ayyukan hadin gwiwa.
“Sama da kashi 58 na basukan kasashen wajen kan karbo su ne ta hanyar jingina, Lamuni ko domin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa.
“An karbo su ne daga masu ba da rance na kasa da kasa irin su Bankin Duniya, Asusun Lamuni na Kasa da Kasa, Bankin Afrexim, Bankin Raya Kasashen Afrika, da kasashen Jamus, China, Japan, India da Faransa.
Ta ci gaba da cewa, har yanzu yawan basukan na kashi 23.06 cikin 100 bai wuce misali ba idan aka kwatanta da yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar.
Ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen vullo da sabbin hanyoyin samun kudaden shiga da kuma rage basukan da ake binta.
A ainihin gaskiya, ya kamata gwamnatin Nijeriya ta san halin da ta ke ciki a game da karuwar bashin da ake bin kasar, domin hakan ya iya jawo wata matsalar, bayan matsalolin da daman kasar ke fuskanta.
Daga Nafisah Awwal, 08141306201
