Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shekara ta 2023 ta zo qarshe, kuma daya daga cikin abubuwan da za a iya cewa a kanta shi ne, shekarar cike ta ke da al’amura masu kyau da munana da suka afku.
Batutuwa kamar tsadar rayuwa, rikice-rikicen ’yan Boko Haram da ISWAP, ’yan bindiga masu satar mutane da kuma rikata-rikitar siyasa sun mamaye yawancin kwanakin shekarar.
Bisa ga dukkan alamu, shekarar 2023 ta zama abar ban tsoro. Za a tuna ta a matsayin shekarar kunci. Hatta Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi ishara da hakan a sakonsa na Kirsimeti, inda ya ce, shekara ce ta kalubalen tsaro da sauran matsaloli, amma ya ce, idan Allah Ya yarda, za a shjga sabuwar shekarar 2024 da kafar dama.
Shekarar 2023 ta zo da kalubale da ’yan Nijeriya, kamar sauran kasashen duniya, tun daga matsalar tsaro da tattalin arziki, matsalar ‘yan ta’adda, hauhawar farashin kayayyaki, wadda ta kara dagula al’amura a kasar. A Nijeriya al’amura da dama sun faru kamar haka:
Harin bom kan makiyaya a Nasarawa:
Akalla makiyaya 27 ne su ka mutu yayin wani harin bom da aka sake musu a ruga a ranar 25 ga watan Janairun 2023.
Lamarin ya faru ne a jihar Nasarawa wanda makiyayan ke zargin harin sama ne da sojoji su ka yi wanda ya raunata da dama.
Daga bisani kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nemi a yi kwakkwaran bincike tare da gano makasudin harin tare da hukunta wadanda ke da hannu a ciki.
29 ga Janairu – Akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon fadowar kwantena daga wata babbar mota kan wata motar haya a Legas.
Zaben 2023 da rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya:
An gudanar da babban zabe a Nijeriya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 inda aka zabi sabon shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa, gwamnoni da ‘yan Majalisar Dattawa da na Wakilai. Ana kallon wannan zabe a matsayin mafi tsauri tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.
An rantsar da sabon shugaban Nijeriya, kasa mafi yawan al’umma da girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Bola Tinubu, mai shekara 71, shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabarairun 2023, tare da alkawarin habaka kasar – duk da cewa akwai jan aiki a gabansa.
Tinubu ya sha rantsuwar ne tare da mataimakinsa Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin kasar.
Sun karvi mulki ne daga Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da kasar ke fama da tashin farashin kayan masarufi da kalubalen tattalin arziki da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Sai dai shugaba mai barin gado, wanda ya kwashe shekara takwas yana mulki ya ce zabe ne mai cike da adalci.
Tinubu wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Legas, na alfahari da rawar da ya taka wajen farfado da jihar, wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta kasar.
Rasa rayuka a lokacin zaben 2023:
Akalla mutane fiye da 100 su ka rasa rayukansu a lokacin zaben shekarar 2023 kamar yadda hukumomi su ka tabbatar. Rahoton ya tabbatar da cewa rasa rayukan sun faru ne tsakanin farkon watan Janairu zuwa 10 ga watan Maris.
Zaben 2023 ya zo da kalubale masu tarin yawa wanda ya jawo rarrabuwar kawuna a kasar ganin yadda zaben ya koma bangaranci da addinanci.
Karasa cire tallafin fetur:
A cikin wannan shekara ta 2023 ne Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kammala cire tallafin man fetur, wanda aka dade a na cece-kuce akansa. Gwamnati mai barin gado ta Muhammadu Buhari ce ta saka dan bar cire tallafin man, inda lokacin da ta amshi ragamar mulki a 2015 man fetur yana Naira 87 kan kowacce lita daya ta mayar da shi Naira 195 kuma ta cire shi daga kasafin kudi na 2023 daga watan Yuni, wato kimanin wata daya bayan rantsuwar da sabuwar gwamnati da za ta gaje ta.
A lokacin jawabin shan rantsuwa ne sabon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa, tallafin man ya tafi kenan.
Rikicin makiyaya da manoma a Nijeriya:
Wasu ’yan bindiga Fulani sun kashe mutum 16 a wani shingen bincike na ‘yan sanda a Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna.
Kisan mutum fiye da mutane 100 a Mangu:
Wani dan majalisar wakilai, Solomon Maren, ya ce, sama da mutane 100 ne ‘yan ta’adda su ka kashe a jihar Filato cikin sa’o’i 48. Maren, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Mangu/Bokkos a yankin Arewa ta Tsakiya, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja. Ya ce kashe-kashen ya faru ne a mazabar sa yayin da aka kai hare-hare a lokuta daban-daban a kauyukan yankin.
Dan majalisar ya ce maharan sun kuma kona gidaje da gonaki da kayayyakin amfanin gona da aka adana, inda ya kara da cewa hare-haren na baya-bayan nan sun kai adadin wadanda suka mutu zuwa 200 a cikin watanni hudu da suka gabata.
16 ga Maris – A wani harin kwantan bauna an yi sanadin mutuwar mutum hudu na ayarin motocin dauke da ‘yan Amurka a jihar Anambra.
Kifewar kwale-kwale a Kwara:
Akalla mutane 100 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwalen dauke da mutanen biki ya kife a kogin Neja a Jihar Kwara.
7 ga Yuli – Jami’an lafiya sun tabbatar da bullar cutar amai da gudawa a babban birnin tarayya Abuja bayan mutuwar wani yaro dan shekara hudu. A cewar NCDC, kusan mutane 800 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar a ranar 30 ga watan Yuni.
2 ga Oktoba – Akalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wata haramtacciyar matatar mai da ke gundumar Emohua a jihar Ribas.
20 ga Oktoba – Yara biyu ne suka mutu yayin da wasu biyu suka jikkata lokacin da wata matsala ta inji ta sa injin kwale-kwale ya kama wuta. Lamarin ya faru ne a garin Katcha da ke Jihar Neja.
29 ga Oktoba – An gano gawarwaki 17, da wasu mutane 73 da suka vata lokacin da wani jirgin ruwa dauke da ‘yan kasuwa da ke dawowa daga kasuwar kifi ya kife a kogin Benuwai. Jirgin na dauke da fasinjoji sama da 100, wadanda aka ceto 14 daga cikinsu.
Hare-haren Jihar Yobe:
Akalla mutane goma sha bakwai ne suka mutu a Gurokayaya da ke Jihar Yobe lokacin da wasu ’yan bindiga da ke goyon bayan Boko Haram suka kai hari kauyen, inda suka far wa mazauna garin da bama-bamai da bindigogi lokacin da aka ce sun ai biyan haraji ga ’yan ta’addan.
31 Oktoba – Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan wata nakiya da ‘yan Boko Haram suka binne ta fashe a lokacin da suke dawowa daga jana’izar wadanda suka mutu daga harin ‘yan ta’adda.
6 ga Nuwamba – Mutane biyu ne suka mutu, wasu biyu kuma suka jikkata a lokacin da wata tanka ta fashe a wajen Babban Hukumar Kanada a Abuja.
Rasuwar Sheikh Giro Argungu:
A ranar 6 ga watan Satumba ce da yammacin aka sanar da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu.
Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau shi ya sanar da rasuwar malamin inda ya tabbatar da cewa Giro ya rasu bayan fama da jinya na tsawon lokaci.
Manya-manyan malaman kasar baki daya sun halarci sallar jana’izar malamin tare da yi masa addu’ar samun rahama.
Mutuwar mawaki Mohbad a Legas:
A ranar 12 ga watan Satumba, Matashin mawaki ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 27 wanda ya girgiza kasar baki daya.
Daga bisani an kama ma’aikaciyar asibitin da ta yi masa allurer ‘Tetanus’ inda rundunar ’yan sanda jihar Legas su ka fara bincike kan mutuwar.
Daga baya an tono gawar Mohbad bayan cece-kuce ya yi yawa kan zargin ba haka kawai ya mutu ba.
Rasuwar Ambasada Nuhu Bamalli:
A ranar 20 ga watan Oktoba ce aka sanar da rasuwar Ambasada Nuhu Bamalli wanda shi ne ya ke rike da Magajin Garin Zazzau.
Marigayin ya kasance dan uwa ga Sarkin Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewacin Nijeriya.
An tabbatar da marigayin ya rasu ne a asibiti mai zaman kanshi a jihar Legas yayin da ya ke shirin tafiya kasar Morocco.
Rusau a Kano:
Tun farkon hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan jihar ya fara rushe wasu gine-gine da ya ke ganin sun sava ka’ida.
Rusau din ya jawo cece-kuce daga cangarorin kasar baki da ma ‘yan kasuwa a jihar da su ke ganin hakan karya tattalin arzikin jihar zai yi.
Daga bisani ‘yan kasuwar sun maka gwamnan a kotu inda a makon da ya gabata kotu ta umarci gwamnan ya biya diyyar biliyan 30.
Amma daga baya Abba Kabir ya amince da biyan biliyan uku kacal ga ‘yan kasuwar a matsayin diyya.
Rasuwar Sheikh Yusuf Ali:
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Shaikh Dokta Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya), ya rasu a daren Lahadi 5 ga watan Nuwamba, 2023, bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.
An yi janaizarsa a ranar Litinin da Azahar a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.
Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alkali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.
Bayan koyarwar addinin da ya dauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta bangaren neman lafiya daga shafar aljanu.
Rasuwar Daraktan Kannywood, Aminu Bono:
Fitaccen Darakta kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Aminu S. Bono ya rasu a ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba.
Mutuwar ta Bono ta girgiza masana’antar wanda aka jima ana jimamin rasuwar.
’Yan uwa da abokan aikin marigayin sun nuna alhini matuka kan rasuwar Bono inda su ka ba da gudunmawa ga iyalansa don rage musu radadi.
Darakta Abdul Amart ya gwangwaje iyalan da sabon gida yayin da kudin hayar gidan da su ke zaune ya kare a lokacin.
Har ila yau, Mawaqi Dauda Rarara ya dauki nauyin karatun ’ya’yansa gaba daya tun farko har karshe.
Kisan ’yan Shi’a:
Nuwamba 16 – ’Yan sanda sun kashe ’yan Shi’a biyu a lokacin wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Kaduna.
Wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Shioro ta jihar Neja ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla goma. An ceto wasu 24 daga wurin.
21 ga Nuwamba – Akalla mutane 25 ne suka mutu sannan kimanin 200 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a babbar titin Yawuri a garin Magama a Jihar Neja.
Harin bam kan masu Mauludi a Tudun Biri:
A ranar Lahadi 3 ga watan Disamba ce rundunar sojin kasa su ka saki bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri dake Jihar Kaduna.
Akalla mutane fiye da 120 su ka mutu inda da dama su ka samu raunuka a Kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin yin bincike tare da daukar mataki kan lamarin da gaggawa.
Wannan lamari ya jawo cece-kuce a aasar da ma kasashen ketare inda kowa ke yin Allah wadai da wannan hari na ganganci.
Har ila yau, kungiyoyi da dama sun yi Allah wadai da wannan harin inda su ka bukaci yin bincike mai tsauri.
Kashe sojoji a Ribas:
13 ga Disamba – Sojoji hudu da direbobi farar hula biyu aka kashe sannan kuma an yi garkuwa da wasu ma’aikatan Koriya ta Kudu biyu a wani harin kwantan vauna da aka kai kan ayarin motoci a Jihar Ribas.
Kisan kiyashi a Filato:
An shiga firgici a ranar Talata 26, 2023, kan hare-haren jajibirin Kirsimeti da aka kai wa al’ummomi a Kananan Hukumomi uku na Jihar Filato.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da ya bayyana mafi muni da aka kai a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na Jihar Filato, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama, inda ya bayar da umarnin a gaggauta kamo wadanda suka aikata kashe-kashen.
’Yan bindigar na cigaba da kai hare-hare a wasu kauyuka, inda sama da mutane 10,000 ne hare-haren suka raba da muhallansu, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga manyan kungiyoyi da daidaikun mutane da suka hada da gwamnonin Arewa da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.
Ita ma aungiyar Amnesty International ta yi kira ga mahukuntan Nijeriya da su binciki duk wani harin da aka kai jihar Filato, tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin.
Amnesty International ta ce, gazawar hukumomi wajen gurfanar da masu aikata irin wannan danyen aiki a gaban kuliya yana qara ta’azzara lamarin.
Rasuwar Hon. Ghali Na’Abba:
A ranar Talata, 26 ga Disamba tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba ya rasu a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. An yi jana’izarsa washegari Laraba a Kofar Kudu dake Fadar Sarkin Kano, Alhaji Amini Ado Bayero, inda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya wakilci tawagar Gwamnatin Tarayya.
Gwamnatin Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasu:
Shekarar 2023 na dab da karewa ne Gwamnan Jihar Ondo ya rasu a safiyar Laraba, 27 ga Disamba Gwamnan Jihar Edo, Oluwa-Rotimi Akeredolu, ya rasu bayan ya sha fama da jinya sakamakon cutar dajin maraina. Gwamnan ya rasu ne a Kasar Jamus yana da shekaru 67.
Rasuwar na zuwa ne bayan kimanin makonni biyu da ya miqa ragamar mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa bayan kai ruwa rana mabiyan marigayin gwamnan. Tuni dai aka rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamna ’yan awanni da rasuwarsa.
