Daga MUHAMMAD SHAMSUDDEN
Na karanta ra’ayoyi mabanbanta a kan wannan maganar, in da mafi yawan masu sharhi suka bayanna rashin gamsuwarsu da wannan tsari. Rubutun da suka fi daukar hankalina a dandalin Fesbuk su ne na Barista Abba Hikima da kuma na Malam Misbahu Baffa Na ‘Yar Talla , ba kawai saboda zurfin iliminsu da hangen nesansu ba, a’a, saboda kokarinsu na tsage gaskiya da rashin siyasantar da abin da ya shafi al’umma. Dukkan wadannan kwararrru sun nuna rashin dacewar wannan tsari, duk da dai dan gajeren rubutu suka yi ba tare da cikakken sharhi ba, watakila saboda suna gudun abinda ka-je ya-zo. Wannan dalili ya sa na ga ya kamata na dan fadada a kan maganar.
Akwai abubuwan da ya kamata mu lura da su kafin yanke hukunci kai tsaye a kan wannan aiki:
- Mu fahimci cewa, kashi 70 na kudin aikin daga kananan hukumomi, ya hada da kudin kananan hukumomin cikin birni guda 8 (wadanda ake ganin su ne za su fi morar aikin) da kuma na wajen birni guda 36. Don haka wannan kudi ba na Yankin kauyuka ba ne kadai. Idan ka hada kudin wadannan da za su fito daga aljihun wadannan guda 8 da Kuma kashi 30 da Gwamnatin Jiha za bayar watakila a yi 50-50 tsakanin cikin birni da wajensa.
- Watakila 36 ta ninka 8 Sau hudu (4), tabbas haka ne, amma idan ka kalli yawan al’umma, wadannan 8 din suna da kusan mutum miliyan 5, yayin da sauran 36 suke da kusan mutum miliyan 11 (kusan 1 : 2 kenan). Wani zai ce “menene hadin yawan jama’a da maganar kudin al’umma?” Akwai dangantaka. Domin kuwa a rabon arzikin kasa na Tarayya (musamman statutory allocation), akan kalli abubuwa Kamar haka: Daidaito 40%, yawan mutane 30%, fadin kasa 10%, samar da kudin shiga 10%, cigaban al’umma10%. Wannan yana da muhimmanci sosai domin mu gane nauyin yawan jama’a wajen rabon tattalin arziki. Wannan ne ma ya saka Jihar Kano take samun kaso mai yawa a rabon arzikin kasar saboda yawan jama’a. Daya dalilin da ya sa Kano take samun kudi daga Tarayya shi ne harajin VAT. Ina iya tunawa a 2021, FIRS ta karvi VAT a Jihar Kano fiye da N24 billion, Wanda haka ya wuce VAT din da gabadayan jihohin Kudu-Maso-Gabas guda 5 suka kawo. Kuma shi dama harajin VAT, fiye da kashi 80 cikin 100 jihohin da kananan hukumomi ake rabawa, Gwamnatin Tarayya kadan take samu a ciki. Yana da kyau mu lura kananan Hukumomin nan guda 8 na cikin gari, za su karbi kudi mai yawa saboda yawan mutane da kuma abinda suke samarwa na haraji fiye da sauran 36. Idan muka ba su 30% (na yawasu) sau 70% (na kudin aiki) zai zama 21% kenan. Wannan shi ne abinda ake tsammani daga kananan Hukumomin 8 na cikin gari kenan. Idan ka hada da kashi 30 na Gwamnatin Jiha, adadin zai kai ka kusan kaso 50% ko fiye.
- Haka kudin shiga na Jiha wato IGR, ma fi yawa yana zuwa ne daga kananan hukumomin cikin gari, Musamman Fagge, Nasarawa, Ungoggo, Kano Municipal, Kumbotso, da wani bangare na Gwale da Dala. Yawanci a nan ma’aikatan Gwamnati da kamfanunuwa suke wadanda suke biyan harajin ma’aikata (PAYE). Sannan harajin kamfani, harajin riba, harajin kasa, da sauransu. Amma haka ake raba IGR din a ba wa kowacce karamar Hukuma, cikin gari da waje, dai-dai misali. Wannan yana da matukar muhimmancin wajen tabbatar da adalci.
- A watan Maris na wannan shekarar, kididdigar Bankin Duniya (World Bank) ta nuna fiye da kashi 53% na ‘yan Nijeriya suna zaune ne cikin birni, kuma WB yana hasashen wannan adadi zai kai kaso 70% daga nan zuwa 2050. Wannan ya tabbatar da cewa mutanen da suke wasu kananan hukumomin suna dawowa cikin gari da zama, kamar Kakannina misali da suka zo kuma suka haife mu. Kuma adadin yana iya karuwa da fiye da kashi 2% cikin 100 kowacce shekara. Wannan yana nuna cewa mutanen da suke kananan hukumomin wajen gari suna amfana kai tsaye da duk wani aiki na ababan more rayuwa a cikin gari. Wannan ba yana nufin abu ne Mai kyau a tattare ayyukan a cikin gari ba, don wannan zai jawo karuwar yawan mutanen da za su bar kauyuka su dawo cikin gari, Kamar yadda Barr Abba Hikima ya fada a rubutunsa. Amma Kuma ba ya nufin kar a fadada kayan more rayuwa na cikin birni har sai kowa ya koma kauyensu tukunna ba.
Na ga shi ma Aminu Rabi’u Tela ya yi irin wannan maganar, kuma a kan hanya take a ganina. Domin hatta wadanda suke zaune a kauyukan, sukan zo cikin gari su yi mu’amala, su koma gida. Kuma suna amfana da irin wadannan ayyukan fiye da wani dan cikin garin ma. Misali, Dakta Gaddafi Sani Shehu ya ce sau 2 kawai ya taba bi ta gadar NNPC dake hotoro, a matsayinsa na dan cikin gari. To na tabbata akwai mutane daga Wudil, Takai, Gaya, Sumaila, da sauransu, wadanda suka fi shi amfani da gadar. Kuma lokacin da ake yin go-slow a wajen kafin Gwamna Ganduje ya gina gadar, sun fi kowa rashin jin dadi da takura.
- Tsarin Federaliya (Federalism) haka ya gada, taimako juna. Man fetur da ake hakowa a Bayelsa, wataqila da kudinsa ake gina titi a Katsina, hakazalika harajin da aka karba a Sokoto sai a yi aiki da shi a Enugu. Haka Tarayya ta gada. Don haka, ba lallai a wannan tsarin a ce kowa iya kudinsa yake mora ba. A baya-bayan nan an ce Gwamnatin Jiha ta ci gaba da aikin titin gezawa. Kuma na ga Gwamnatin ta sayi motocin ambulance guda 44 ta raba wa dukkan qananan hukumomi ba tare da duba yawan kudin da suke samarwa ba ko kuma yawan al’ummarsu. An ce ma an ci gaba da ayyukan 5 kilomita a wasu guraren. Kuma babu wanda ya yi ƙorafi. To haka Tarayya take. Wani lokacin ma mutum daya za a ware a kashe masa kudi mai yawa, misali daliban da aka kai su karatu kasar waje, ko Kuma Yarinya da aka biya wa kudin tiyata. Ba yadda za a yi, haka tsarin yake. Kuma ba zalunci ba ne, ta wannan fuskar (a ganina).
- Abinda kawai za a tambaya shi ne: “shin aikin gada mutanen Kano suke buqata a yanzu?” Amsar Wannan kuma kowa da ra’ayinsa, kuma yana da damar bayyana shi. Ni a ganina, wannan kudin biliyan 16, idan aka yi kananan titina, kamar guda 100 akan kudi naira miliyan 160 kowanne daya, a birni da kauyuka, sai ya fi taimakon al’umma. Alabashi ita kuma gadar, nan gaba sai a yi ta a hankali. Amma fa wannan ra’ayina ne. Duk da dai ina fatan aikin gada kadai ba zai hana sauran ayyukan da ya kamata Gwamnati ta yi ba, a birni da qauye.
- Duk inda matsalar take shi ne da aka kyale Gwamnoni suka yi babakere akan asusun kananan hukumomi. Shekara kamar 2 da ta wuce, Tsohon Shugaban Kasa Buhari, ya yi yunkurin gyara wannan matsalar, amma Gwamnoni da Majalisun Jihohi, suka yi kememe, suka kawo wa dokar tarnaki, shi kuma Shugaban kasar ya hakura saboda rashin jajircewa. Irin wannan gyaran, shi kadai ne zai yi maganin irin wannan cece-kuce. Kowacce karamar hukuma a ba ta sadakinta a hannunta; illa iyaka.
Shamsuddeen Muhammad ɗan siyasa ne kuma mai sharhi kan lamurran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.
