Yadda Kirista ya ɓoye wata Musulma ta haifa masa yara uku a Zariya – Kwamandan Hizbah

Spread the love

Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya

Rundunar tsaro ta Hizbah a Karamar Hukumar Sabongarin Zariya a Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wani Kirista da ya boye wata yarinya Musulma na tsawon shekara bakwai.

Babban kwamandan Hizbah a karamar hukumar Sabongari, Alhaji Abubakar Auwal Adam ya shaida wa wakilinmu haka a lokacin da ya zanta da shi a cibiyar karamar hukumar Sabongari da ke Dogarawa.

Alhaji Abubakar Auwal ya ci gaba da cewar, sun samu nasarar damke mutumin ne mai suna Mista Joe bayan sun dauki dogon lokaci suna gudanar da bincike bisa rahoton sirrin da su ka samu daga ma’aikatansu.

Mista Joe bayan shiga komar ‘yan Hizbah a cewar Alhaji Abubakar Adam, ya ce ya hadu da matashiyar ce a wani gidan man fetur a Dogarawa, Sabongarin Zariya inda ya ga yarinyar, ya ce ya tambayeta ina za ta, sai ta nuna masa Kano za ta tafi, sai ya ce mata dare ya yi, yana da inda za ta kwana, sai gobe ta wuce.

A cewar Joe, tun daga ranar da ta shiga gidansu, ya sa ta a daki, ba ta taba fitowa kofar gidan ba, ya ce da zarar ta samu juna biyu har gida ya ke gayyato masana kiwon lafiya, su taimaka mata ta haihu.

Alhaji Abubakar ya tabbatar da cewar, mahaifin Joe ya shaida ma su cewar, tun farko ya bukaci ya fita da wannan yarinya a cikin wannan gida, dan ya ki umurnin mahaifin, a karshe har mahaifin ya samu lallurar makanta, bai san yarinyar na nan ko ba ta a gidan.

Kwamandan rundunar Hizbah a Sabongari ya tabbatar da cewar, shekara bakwai da voye wannan yarinya da Joe ya yi, haihuwar farko, ta haifi namiji sai na biyu ta haifi tagwaye mace da na miji.

Zuwa haxa wannan rahoton, shugaban Hizbah ya ce suna nan suna ci gaba da binciken wannan matsala, da zarar sun kammala, za su dauki matakin da ya dace.

Alhaji Abubakar Adam ya kammala da jinjina ga majalisar karamar hukumar Sabongari bisa shugabancin Injiniya Mohammed Usman na yadda suka yi doka mai karfi da ya sa Hizbah ke aiwatar da ayyukansu a cikin sauki.

By Editor