Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya yo alkawarin cewa sabuwar kwangilar da aka rattaba tsakanin Gwamnatin Nijeriya da kamfanin Siemes Energy na Jamus, zai gaggauta samar da wadatacciyar wutar da aka dade fiye da shekaru talatin ana mafarkin samu, amma hakan ya gagara.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a cikin jawabin murnar shiga sabuwar shekarar 2024 da ya yi a safiyar Litinin.
“A lokacin Taron COP28 a Dubai, Shugaban Jamus Olaf Scholz da ni mun amince mu gaggauta shirin samar Siemens Energy Power na aikin samar da wadatacciyar wutar lantarki a fadin Nijeriya, wanda aka fara tun 2018,” inji Tinubu.
Gwamnatocin baya sun sha yin alkawarin gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla, amma maganar na shiriricewa.
Ko gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wa ‘yan Nijeriya alkawari za ta gina tashar samar da wutar lantarkin Mambilla, amma maganar ta zama tatsuniya.
Ko cikin makon shekaranjiya sai da EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan da ta ke farauta, bayan ya mika kan sa da kan sa.
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, wanda EFCC ta buga cigiya da farautar sa a makin da ya gabata, zai gurfana gaban kotu, bayan shafe kwanaki biyar a tsare a hannun jami’an hukumar.
Olu Agunloye zai fuskanci shari’a bayan shafe kwanaki biyar a hannun EFCC.
Ya mika kan sa da kan sa a hannun jami’an EFCC a ranar 13 ga Disamba, kwana daya bayan an buga cigiya da farautar neman sa ruwa a jallo, a duk inda ya ke.
Ana zargin sa dangane da karkatar da kudade a wata kwangilar biliyoyin dalolin aikin wutar Mambilla, kwangilar da ba a yi aikin ba.
An bayyana cigiya da neman sa ne bayan an ba shi belin kan sa, amma daga baya ya ki kai kan sa ofishin hukumar.
Agunloye ya yi Ministan Makamashi a zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Cikin makon jiya ne dai EFCC ta bayyana cigiya da farautar tsohon ministan kan yi wa dala biliyan 6 ‘yar-burum-burum a kwangilar aikin samar da wutar lantarki a Mambilla, aikin da kwata-kwata ba a yi ba.
Kafin ya kai kan sa da kan sa, Hukumar EFCC ta bayyana cigiyar tare da farautar tsohon Ministan Makamashi da karafa, Olu Agunloye.
EFCC na cigiyar Agunloye ne bisa zargin harkalla da kuma buga takardun bayanai na boge a kwangilar aikin wutar lantarki ta Mambilla.
An zargi tsohon ministan da yin daka-dakar bayar da kwangilar aikin wutar lantarki ta dala biliyan 6, a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, ba tare da tuntuvar Gwamnatin Tarayya ba.
EFCC ta bayyana cigiya da farautar tsohon ministan a cikin shafin ta na Instagram da kuma Facebook.
A cikin sanarwar, an buga hoton sa, tare da bayyana shekarun sa 75.
Hukumar EFCC ta roki duk wani wanda ya gan shi ko ya san inda ya ke, to ya tuntuvi ko da daya ne a cikin ofisoshin hukumar da ke Benin, Kaduna, Ibadan, Sokoto, Maiduguri, Makurdi, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Uyo, Fatakwal ko na Abuja.
Kakakin EFCC Oladele Oyewale bai yi cikakken bayani dangane da irin nauyin zarge-zargen da ake yi wa Agunloye ba.
Cikin watan Satumba Agunloye ya fito ya ce a baya EFCC ta bincike shi, har ma ta tsare shi, dangane da batun kwangilar.
Ya yi wannan furuci ne bayan tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi hira da jaridar The Cable, inda ya ce tsohon Ministan Makamashi da karafa a lokacin da, Olu Agunloye ya bayar da kwangilar aikin wutar Mambilla, ba tare da amincewar Majalisar Zartaswa ta kasa ba.
Da farko an bayar da kwangilar wutar lantarkin Mambilla, ga wani kamfani wai shi Sunrise Power and Transmission Limited a cikin 2023.
Obasanjo ya yi kokarin nesanta kan sa daga harkallar kwangilar, inda ya ce shi bai ma san lokacin da Agunloye ya bayar da kwangilar ba.
