Daga BASHIR ISAH
Al’umma mazauna Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun shiga firgici da tashin hankali biyo bayan fashewa mai karfi da ta auku da yammacin Talata a birnin.
Mazauna yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da sauransu sun ce, hatta gidaje da wasu motocin da ke kusa sai da suka amsa sakamakon karfin fashewar.
A wani sako da ta wallaffa a shafinta na X, Gwamnatin Jihar Oyo ta ce ta samu rahoton fashewar da ta auku.
“Ana kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kasancewar hukumomin tsaro sun sunkuya bincike domin gano musababbin fashewar,” in ji Gwamnatin Jihar.
Jaridar News Point Nigeria ta rawito an samu asarar rai da ba a tancetance adadi ba sakamakon fashewar, haka ma dukiya mai yawa ta lalace.
Majiyarmu ta ce asibitocin yankin sun cika da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar ana yi musu magani.
Kwamishinan Labarai da Wayar da Kai na Jihar, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar cewa ana kan kula da lamarin yadda ya kamata.
Ya ce, “Mazauna Ibadan da kewa sun shaida fahewar da ba a saba ji ba da misalin karfe 8:00 na dare.
“Gwamna Seyi Makinde ya bukaci jama’a kowa ya kwantar da hankali, tare da bada tabbacin za a yi abin da ya dace don amfanin jana’a.”
