Da Ɗumi-ɗumi: Mutfwang ya kafa dokar hana zirga-zirga a wani sashen Filato

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a yankin Karamar Hukumar Mangu da ke jihar.

MANHAJA ta rawaito jafa dokar wadda ta fara aiki ne nan take, na da nasaba da harin da aka kai yankin da ke Sabon Gari a Mangu cikin daren Litinin da ta gabata lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da ba bayyana adadinsu ba.

Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Sakataren Yada Labarai a Ofishin Gwamna, Gyang Bere, ya ce Gwamna Mutfwang ya dauki matakin kafa dokar ne bayan da ya tuntubi hukumomin tsaron jihar.

Ya kara da cewa, ma’aikata masu ayyuka na musamman ne kadai aka lamunce wa yin zirga-zirga yayin da dokar ke ci gaba da aiki.

Sanarwar ta kuma bukaci al’ummar jihar musamman na yankin Karamar Hukumar Mangu, da su kiyaye wannan doka saboda jami’an tsaro na nan na yawo don hukunta duk wanda suka kama da laifin bin dokar.

By Editor