Ɗan jari-bola ya tsunto bom da ya tashi da almajirai a Borno

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani abun fashewa ya kashe wasu almajiran wata makaranta hudu tare da wasu mutum biyu da ba a gano su wane ne ba a Karamar Hukumar Gubio da ke Jihar Borno.

An ruwaito cewa, shugaban aaramar hukumar Alhaji Mali Gubio ne ya tabbatar mata da faruwar wannan lamari, ya ce abin ya fashe a wani kango da misali qarfe 11 na safiyar Asabar.

“Duka mutanen da abin ya rutsa da su sun mutu, don haka ba za mu iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma wani abun fashewa ne ya tashi a inda ake ajiye matattun karafa.”

“An gano gawar wasu almajirai huɗu, da wasu manyan mutane biyu sai dai ba mu kai ga gane daga ina suke ba, babu kuma wanda ya zo ya ce ’yan uwansa ne,” inji shi.

Tuni gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya haramta gwangwan a jihar saboda lalata kayan gwamnati da sunan gwangwan.

By Editor