NAHCON ta bayyana kuɗin Hajjin bana

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta  bayyana adadin kudin da maniyyata za su biya domin aikin Hajjn 2024.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Asabar ta bakin mai magana da yawunta, Fatima Sanda Usara, NAHCON ta ce game da Hajjin bana maniyyata daga Kudancin Nijeriya za su biya Miliyan N4,899,000, yayin da maniyyata daga Arewacin kasa za su biya Miliyan N4,699,000.

Sanarwar ta kara da cewa, maniyyata daga Yola da Maiduguri Naira Miliyan 4,679,000 ne za su biya a matsayin kudin Hajjin 2024.

Kafin wannan lokaci, Shugaban NAHCON na Kasa, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya yi hasashen ko abin da aka biya bara shi za a sake biya a bana wanda hakan ya sa hukumar ta bukaci maniyyatan bana da su fara biyan Miliyan N4.5 kafin ganin abin hali ya yi.

Hukumar ta ce karin da aka samu na da nasaba da yadda farashin Dala ya cilla sama a kasuwar canji wanda hakan ya haifar da karin da ya auku duk da kokarin da NAHCON karkashin jagorancin Jalal Ahmad ta yi don ganin ba a samu kari.

A kwanan nan an ga yadda Mala Arabi da tawagarsa suka ziyarci Saudiyya innda suka tattauna da bangarorin da lamarin ya shafa wajen nema wa mahajjatan Nijeriya saukin kashe kudi yazu aikin Hajjin da ke tafe.

A cewar sanarwar ba domin fadi-tashin da NAHCON ta yi wajen nema wa Nijeriya rage kashe kudi wajen yi wa mahajjatanta hidima yayin aikin Hajji a saudiyya ba, da watakila abin da maniyyatan bana za su biya sai ya kai kimanin Miliyan N6,000,000.

By Editor