Gwamna Idris ya yi wa yaran da ba sa zuwa makaranta rajista a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kira taron ilimi na dukkan masu ruwa da tsaki a fannin ilmi don karfafa dabarun bunqasa ilimi da cigaban ilimi a jihar Kebbi. 

Ya bayyana haka ne a wajen bukin kaddamar da rabon kayayyakin ilimi ga yaran da ba su zuwa makaranta a garin Birnin Kebbi a ranar Talatar da ta gabata. 

Ya bayyana cewa bayan rantsar da wannan gwamantin kawo yau ta kashe sama da Naira biliyan tara wajen samar da yanayi mai kyau a makarantu da suka hada da gyare-gyare da gina azuzuwa, samar da kayayyakin koyarwa ingantattu na koyo da koyarwa, da kuma kula da jin dadin malamai.

“A matsayina na qwararren malami, na san matsalolin malamai da koyarwa saboda haka yana daga cikin kudurorina na ganin na bai wa jin dadin malamai  muhimmanci saboda a faranta musu rai domin samun yanayin aiki mai kyau,” inji shi.

Gwamna Idris ya ce kuma in Sha Allahu ba da dadewa ba gwamnatin jihar Kebbi za ta dauki kwararrun malamai da za su koyar a makarantu kamar yadda tsarin ilimi ya tanada saboda shi tsohon shugaban kungiyar malamai ta kasa NUT ne kuma shi mamba ne kai tsaye a Majalisar Registration Council, TRC.

Gwamnan ya sanar da taron cewa gwamnatin jihar ta samu nasarori a makarantun da ta rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta, wanda ya sanya jihar Kebbi a cikin jihohi 17 da ke kan gaba wajen samun karuwar irin wadannan yara.

Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa ga bullowa da shirin “Better Education Delivery for All, BESDA, don rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta a kasar nan, haka nan kamar yadda ya yabawa Karamin Ministan Ilimi Hon Tanko Yusuf Sununu bisa yadda ya taimaka a fannin ilimi a jihar Kebbi.

A ci gaba da daukar yaran da ba su zuwa makaranta, Gwamna Nasir Idris ya yi wa Salim Sirajo rijista da Firdausi Usman. su shiga tsarin ilimi na boko, tare da basu kayan karatu da suka kunshi tufafin makaranta da littattafai da kayan rubutu.

A nasa jawabin karamin ministan ilimi Hon Tanko Yusuf Sununu ya yabawa gwamna Nasir Idris bisa gagarumin cigaban ilimi da cigaban jihar Kebbi da sauran vangarorin da suka inganta rayuwar al’ummar jihar Kebbi.

Ministan ya bayyana adadin yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya, wanda aka kiyasta kimanin miliyan goma zuwa ashirin a matsayin abin damuwa, inda ya bukaci gwamnatocin jihohi a fadin kasar nan da su hada hannu da gwamnatin tarayya domin shawo kan matsalar.

Hon. Sununu ya roki Gwamna Kauran Gwandu a matsayinsa na mai rike da sarautar gargajiya da ya hada kan sarakunan gargajiya domin a dawo da martabar malamai ta hanyar shigar da manyan malamai wajen yanke hukunci a dukkan al’umma na birni da karkara.

Shugaban Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar, SUBEB, Farfesa Suleiman Khalid Jega, ya yi tsokaci tare da kididdiga, na nasarorin ilimi da gwamnatin Kauran Gwandu ta samu inda ya bayyana cewa jihar Kebbi ta dauki matsayi na daya a cikin jihohi 17 da ke aiwatar da shirin BESDA, wanda aka tsara don mayar da yaran da ba su zuwa makaranta aji.

By Editor