Yadda bikin ‘yar marubuciya Bilkisu Ali ya ƙayatar

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

An daura auren Sarra Tasi’u Ya’u Babura ‘yar marubuciya ‘yar Jarida kuma malama a Jami’ar Alqalam Hajiya Bilkisu Yusuf Ali tare da yin tarukan biki na kece raini.

An daura auren Sarra Tasi’u Babura da angota Salihu Ibrahim Darma (Khalifa) ne dai a ranar Juma’a 9 ga Fabarairu 2024 ne a gidan Imam Sheikh Dr. Yusuf Ali da ke Unguwar Tudun Maliki ta Karamar Hukumar Kumbotso a cikin garin Kano da misalin 2-30 na rana inda dumbin jama’a suka halarci daurin auren.

Bayan daurin auren ne kuma uwar amarya ta shirya taron wuni a wajen taro na Darru Tauhid da ke titin Zariya in da ‘yan uwa suka hadu suka taya ta murna domin zuwan wannan rana ta bikin ‘yarta Sarra Tasi’u Ya’u Babura.

A ranar Asabar kuma kwana guda da daurin auren an shirya wata babbar liyafa ta cin abinci don taya ango da amarya murna.

Sai dai wannan liyafar da Bilkisu Yusuf Ali ta shirya za a iya cewa ta kece raini ce, domin kuwa wani taro ne da aka shirya na gani na fada, don haka shi kansa wajen da aka yi taron bikin sai da aka zavi waje na alfarma, yayin da su kansu mahalarta taron bikin mutane ne da suke da matsayin da kuma daraja a wajen Bilkisu Yusuf Ali.

An dai shirya taron ne a Preme Event Center da ke titin Hadeja. An shirya wajen zama na kowanne rukuni na masoyan uwar amarya da ‘yan uwa da kuma kawaye da abokan aiki marubuta an shirya musu wajen zaman su daban su ma sai da aka ware wajen zaman marubuta maza da kuma marubuta mata.

Kungiyar ‘yan fim mata da suka halarci wajen a karkashin jagorancin Hauwa Edita su ma wajen su daban, haka su ma abokan karatun ta na sakandaren Gwauron Dutse su ma wajen su daban.

Sai kuma babbar gayya iyalan marigayi Sarkin malaman masarautar Gaya Imam Sheikh Dr. Yusuf Ali tare da danjin miji su ma wajen su daban.

An dai fara bikin da misalin karfe 9 na dare a lokacin da tawagar uwar amarya ta shigo dakin taron tare da rakiyar marubuta mata. Umma Sulaiman ‘Yan awaki ta bude taron da addu’a, yayin da ita kuma marubuciya Hadiza Nuhu Gudaji ta yi jawabin maraba.

Sai kuma amarya ta shigo tare da rakiyar kawayen ta da dangin miji, sannan shi ma ango ya shigo bisa rakiya abokan sa, daga nan kuma aka shiga shagalin biki.

An yi biki da birede an cashe iya son rai, sannan an ci an sha an yi hani’an abin da sai wanda ya halarci taron zai iya tabbatar yadda taron ya dauki hankalin mutane tare da burge su.

Da fatan Allah ya sanya albarka a cikin wannan aure ya bada zaman lafiya da zuriya tagari.

By Editor