Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta sanar da shirya zanga-zangar gama-gari na yini biyu domin nuna rashin jin daɗinta dangane da tsadar rayuwar da ake fuskanta a Nijeriya.
Ƙungiyar ta ce za ta gudanar da zanga-zangar ne a ranakun 27 da 28 ga Fabrairun 2024.
Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan yayin taron gaggawar da ƙungiyar ta shirya ranar Juma’a a babban ofishinta da ke Abuja.
Joe ya ce, “Abin da takaici tura mu da aka yi zuwa ga ɗaukar wannan mataki, sai dai ci gaba da yin biris da ake yi game da walwalar ‘yan Nijeriya da kuma ƙuncin rayuwar da aka jefa talakawa ya sa ba mu da wani zaɓi wuce wanda muka ɗauka.”
Ya ƙara da cewa, an yanke shawarar shiraya zanga-zangar ne bayan cikar wa’adin kwana 14 da aka bai wa Gwamnatin Tarayya kan ta kawo ƙarshen wahalar da ‘yan ƙasar ke fuskanta.
Bayanan baya-bayan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar sun nuna cewa, farashin kayayyakin masarufi ya ƙaru zuwa 29.90 a watan Janairun bana yayin da darajar Naira ke ci gaba da faɗuwa.
