‘Yan bindiga sun kai hari hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zamfara, sun kashe DCO

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu gungun ‘yan ta’adda ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Zurmi, hedikwatar karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a Lahadin da ta gabta.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Lawali Zurmi, ya tabbatar da faruwar harin ga wakilinmu a hirarsu ta wayar tarho.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda reshen ƙaramar hukumar inda suka banka ma ofishin wuta.

“Kamar yadda nake magana da kai, yanzu an ƙona ofishin ‘yan sanda na sashinmu kuma yawancin jama’a sun gudu don kare lafiyarsu,” in ji shi.

Wakilinmu ya tattaro cewar ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yammacin Lahadi.

“Kuma zan iya gaya muku cewa muna iya ganin su ɗauke da miyagun makamai bisa babura suna tururuwa zuwa cikin garin daga inda muke a ɓoye a cikin daji”.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa harin bai rasa nasaba da yadda ’yan banga da ke yankin suka haɗa kansu tare da kai farmaki kan wasu daga cikin ‘yan bindigar a inda suke a kwanan baya inda suka kashe mutanen su huɗu tare da kama ɗaya daga cikin ɓarayin.

An kuma tattaro cewa a lokacin da ‘yan banga suka kama ɗan bindigar, daga bisani sun kashe shi, lamarin da ya sa jama’arsu suka kai harin ramuwar gayya kan al’ummar yankin.

MANHAJA ta gano cewa yayin harin, ‘yan bindigar sun kashe jami’in ‘yan sanda mai kula da manyan laifuka, DCO, tare da wasu jami’an ‘yan sanda da dama sun samu munanan raunuka, inda daga bisani suka bankawa ofishin ‘yan sandan wuta.

‘Yan bindigan da suka ga sojoji sai suka tsere zuwa daji kuma duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Asp Yazid Abubakar ya ci tura saboda duk layinsa basu zuwa.

By Editor