Daga DAUDA USMAN a Legas
Waɗansu sababbin tagwayen sarakunan al’ummar Hausawa mazauna cikin garin Muwe da ke cikin jihar Ogun sun bayyana cewar za su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kare martabar masarautar al’ummar Hausawan Muwe tare da kawo ci gaban Hausawan yankin baki ɗaya.
Sababbin sarakunan sun yi wannan furuci ne a garin Muwe jim kaɗan bayan tashi daga taron naɗa su muƙamai daban-daban a cikin garin Muwe kuma suka bayyana wa jaridar Manhaja farin cikinsu dangane da wannan al’amari.
Taron naɗin sarautun wanda ya gudana a garin na Muwe a ranar Lahadin makon jiya sunayen sababbin tagwayen sarakunan da majalisar Sarkin Hausawan na garin Muwe ta naɗa wanda suka haɗa da Alhaji Abdullahi Muazu matsayin hakimin Agoyere da Faruku Umar Sarkin Yaƙin garin Muwe da Mohammed Sani Abubakar Fele a matsayin Shamakin Sarkin Hausawan Muwe.
Da yake ci gaba da nuna farin cikinsa dangane da wannan sarauta da Allah ubangiji ya bashi Alhaji Abdullahi Mu’azu hakimin na Agoyere inda bayan ya kammala gabatar da muhimman jawabansa a wajen taron ya cigaba da isar da saqon godiyarsa ga dukkan al’ummar da suka sanya bakunansu da hannuwansu da ma aljihunsu yana yi wa kowa fatan alheri, haka kuma za su yi iyakar ƙoƙarinsu su ga cewar sun kawo ci gaban fadar mai martaba Sarkin Hausawan Muwe Alhaji Bello umar da hausawan garin muwe gaba ɗaya shima a nasa tsokacin a wajen taron Faruku umar Sarkin Yaƙin garin Muwe gaba ɗaya bayan ya kammala isar da ta sa godiyar ga Allah Ubangijin suba hanahu wata ala da ya ba shi iKo tare da izinin ganin wannan rana da fadar Sarkin Hausawan Muwe tana da shi matsayin sarkin yaƙin Muwe gaba ɗaya.
Ya ce yana yi wa sarki da ‘yan majalisun shi godiya bisa ga wannan al’amari ya ce kuma za su yi iyakar yadda za su yi a wajen kawo zaman lafiya tare da cigaban fadar sarkin Hausawan Muwe gaba daya shima da yake gudanar da nasa jawabin a wajen taron.
Mohammed Sani Abubakar Fele bayan ya kammala nuna jin daɗinsa a game da wannan sarauta da Allah Ubangiji ya ba shi ya ci gaba da nuna gamsuwarsa ga jagorancin Sarkin Hausawan na garin muwe Alhaji Bello Umar ya ce kuma za su yi iyakar yadda za su yi a wajen kare mutuncin fada da al’ummar Hausawan garin Muwe da ma na jihar Ogun gaba ɗaya.
Ƙarshe ya ce yana yi wa Nijeriya fatan alheri na ci gaba da samun zaman lafiya.
