Daga BASHIR ISAH
Wasu mazauna yankin Abuja sun kai mamaye rumbun ajiyar kayan abinci mallakar Hukumar Bada Agajijn Gaggawa ta Nijeriya warehouse belonging (NEMA).
MANHAJA ta kalato hakan ya faru ne da safiyar Lahadi a yankin Karimo, Phase 3.
Rahotanni sun ce mutane sun kwashi kayayyakin abinci da dama waɗanda ke ajiye a rumbun.
Hakan ba ya rasa nasaba da ƙuncin rayuwar da ake fuskanta a ƙasa wanda ya kai ga sayen abinci na gagara talakawa saboda hauhawar farashi.
