…Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ruwan wuta a Katsina da Zamfara
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
An sace ɗaliban firamare da na sakandare sama da 100 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Kawo yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace, amma mazauna yankin sun ce kusan 100 ne.
Rahotanni sun ce shugaban makarantar da wasu ma’aikatan makarantar na cikin waɗanda abin ya shafa.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe a lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) na ranar Alhamis.
Ɗaliban sakandare sun koma ginin makarantar da ke cikin garin Kuriga a shekarun baya saboda rashin tsaro, inda suka yi watsi da tsohon ginin makarantar da ke wajen garin.
Wani mazaunin garin Shitu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce galibin ɗaliban sun tsere daga ajijjuwan su a lokacin da suka hango ’yan bindigar a harabar makarantar.
Shi ma wani mazaunin garin Lawal Kuriga ya shaida wa manema laabarai cewa an garzaya da waɗanda aka sace zuwa cikin dajin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar domin kwamishinan sa ido na ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, bai mayar da martani kan sakon da aka aike masa ba.
An kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ta wayar tarho kuma har yanzu bai amsa wani saƙo da aka aike masa ba.
A ɗaya hannun kuwa, a jiya Alhamis ne Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF) ta hannun dakarun Operation Hadarin Daji ta kai hari matsugunan ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina, inda suka kashe ’yan ta’adda da dama.
Hakan na qunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NAF Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, hare-haren da aka kai a ranar 5 ga Maris, 2024, an kashe ‘yan ta’adda a tungar fitaccen shugaban su, Maudi Maudi, da kuma wasu kwamandojin ’yan ta’adda da ke kudu da Tsaskiya a ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina.
“An kai hare-haren ne ta hanyar sa ido da kuma ayyukan leƙen asiri da aka gudanar a yankin da aka yi niyya inda aka ga tarin bukkoki da aba gane musu a tsakar daji.
“Binciken ya kuma tabbatar da kasancewar ‘yan ta’adda ɗauke da muggan makamai da ke tururuwa a cikin bukkokin, bayan haka an samu izinin kai farmakin.
“Binciken da aka yi bayan harin ya nuna inda aka yi niyya na ci da wuta, inda aka ga wasu tsirarun ‘yan ta’addan suna gudu domin neman tsira. Ko da yake an kawar da ‘yan ta’adda da dama, har yanzu ba a tabbatar da cewa Maudi Maudi na cikin waɗanda aka kashe ba,” inji shi.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa an kuma kai irin wannan harin a ranar 6 ga Maris, 2024 a tungar fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Alhaji Na-Shama, da ke gabashin aauyen Ussu a cikin gundumar Nasarawar Mailayi a ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.
An lura cewa amintattun bayanan sirri na ɗan adam sun tabbatar da halakar da yawa daga cikin mayaƙan Na-Shama tare da rusa sansaninsa da ke dajin.
