Farfesa Suleiman na NSUK ya taka rawar gani – Dokta Suleiman

Spread the love

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Shugaban Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya na Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Dokta Abdullahi Suleiman Mohammed, ya ce babu shakka takwaransa na Jami’ar Jihar (NSUK), wato f’Farfesa Suleiman Bala Mohammed, ya taka rawar gani wajen haɗa kawunan shugabannin manyan makarantun da ke faɗin Jihar.

Dokta Suleiman ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a ofishin sa dake kwalejin ranar Laraba ta wannan makon

Ya ce Farfesa Suleiman wanda wa’adin mulkin sa zai ƙare a watan Maris da ake ciki, kafin yanzu ya yi ƙoƙarin haɗa kawunan takwarorinsa don ci gaban fannin ilimi da ma jihar baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, shugabannin manyan makarantun za su yi kewar Farfesa Suleiman bayan kammala wa’adin aikinsa.

A cewarsa, ba su shugabannin manyan makarantun ne kaɗai za su yi kewar Farfesan ba har da fannin ilimin jihar da ma gwamnatin jihar baki ɗaya.

Haka nan, ya Dokta Suleiman ya taɓo wasu daga cikin ɗimbin ayyukan inganta ilimi da Farfesa Suleiman Bala ya aiwatar a jami’ar kafin yanzu da suka haɗa da jawo ra’ayin Gwamnatin Tarayya ta hukumar TetFund inda aka ta yin gine-ginen azuzuwa da sauran fannonin karatu daban-daban a jami’ar.

Daga nan, Dokta Abdullahi Suleiman ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa takwaran nasa mai barin gado fatar alheri a harkokin rayuwar sa na gaba inda ya buƙace shi da ya ci gaba da ba da kyawawar gudumawa kamar yadda ya saba ga ɓangaren ilimi a duk inda ya tsinci kansa.

By Editor