Daga BASHIR ISAH
Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rancen karatu ta 2024 wanda ɗalibai a manyan makarantu za su ci gajiya.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan da ta karɓi rahoton Kwamitin Majalisar kan Manyan Makarantu da asusun
TETFUND.
Shugaban Kwamitin, Sanata Muntari Dandutse (APC – Katsina ta Kudu), shi ne ya gabatar da rahoton yayin zaman malajisar a ranar Laraba.
Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dattawa da ta wakilai buƙatar neman soke dokar bai wa ɗalibai rancen karatu (ga ɗaliban manyan makarantu), da kuma kafa wata sabuwa.
Ana sa ran sabuwar dokar za ta taimaka wajen aiwatar da Shirin Bai wa Ɗalibai a Manyan Makarantu Rancen Karatu ta hanyar kawar da ƙalubalan da ke tattare da shiri Nigerian Education Loan Fund (NELF) da sauransu.
Wannan mataki da Tinubu ya ɗauka na zuwa ne bayan sanar da dakatar da fara aiwatar da shirin bai wa ɗalibai rance na wucin gdi.
An samar da wannan doka ne domin bai wa ɗaliban Nijeriya a manyan makarantu damar samun rance mai sauƙin ruwa da zai taimaka musu a sha’anin karatunsu.
