Muƙamin Matawalle a matsayin ministan tsaro bai amfana wa Zamfara komai ba — Gwamna Lawal

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce jihar ba ta ci gajiyar nadin da aka yi wa magabacinsa, Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani shiri na kai-tsaye a gidan Talabijin na Channels Television na Sunrise Daily a ranar Talata.

“Abin mamaki ne ko yaushe idan wannan batu na Ministan Tsaro ya taso. Eh, shi ne Karamin Ministan Tsaro, amma me ya amfana mana? Kimanin makonni kadan da suka gabata ne ‘yan bindiga suka je garinsu, suka kashe mutane da dama, me ya yi akai?

“Eh, muna da ministan tsaro, amma wace riba jihar Zamfara za ta samu?,” in ji shi

By ukarofi