
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa kan yadda jami’an ‘Yan Sanda ke bijire wa karɓar umurni ta hanyar da doka ta tsara inda take zargin wasu mutane da ba huruminsu bane ke juya hukumar.
Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na Jihar, Haruna Isa Dederi ya faɗi hakan a wani taron manema labarai inda ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne shugaban harkar tsaron Jihar kuma ke da ikon umurtar dukkan hukumomin tsaron Jihar.
Dederi ya ce, wasu mutane da ba a san ko suwaye ba suna bada umurni ga hukumar ‘Yan Sanda inda ya bada misali da batun soke bukukuwan sallah da ta yi kwanaki kaɗan da suka wuce yayin da ya ce basu shawarci gwamnan ko cibiyar harka tsaron Jihar ba.
Ya ƙara da cewa, “ya za’a yi a ce an dakatar da bukukuwan sallah a Kano? Yaushe aka sauke gwamnan a matsayinsa na shugaban harkar tsaron Jihar da sai dai ya ga sanarwar hakan na yawo a kafafen sada zumunta? Wa ke zuga kwamishinan ‘Yan Sanda ƙin martaba matsayin gwamnan?” Inji Dederi
Daga ƙarshe, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne shugaban harkar tsaron Jihar kuma ke da damar tabbatar da tsaron rayuka da dokiyoyin al’ummar Jihar a hukumance.
