
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, (CAF) ta ce za’a gudanar da gasar cin kofin Nahiyar Afirka, (AFCON) a tsakanin 21 ga watan Disamba, 2025 da kuma 18 ga watan Janairun 2026 wanda za’a yi a ƙasar, Moroko dake Arewacin Afirka.
CAF ta yanke hakan ne, a yayin wani zaman manyan ofisoshinta da ta saba yi, a ranar juma’a inda ta ce da ta so gudanar da gasar a lokacin bazara ne a cikin shekarar 2025, amma saboda ya haɗu lokacin gasar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta duniya, sai ta mayar da shi zuwa ƙarshen shekarar.
Za’a gudanar da taron shirya jadawalin wasannin a watan Yulin shekararnan, a birnin Johannesburg dake ƙasar Afirka ta Kudu.
Sannan kuma, a watan Satumba zuwa Oktoban 2024 ne za’a buga wasannin hayewa zuwa zagayen rukuni-rukuni na gasar.
