Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira biliyan bakwai wajen gina cibiyar tiyatar zuciya a Dutse

Spread the love


Daga Umar Akilu Majeri Dutse

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware naira Biliyan biyu da naira miliyan dari Tara da tamanin da daya N2,981,000 wadda za a gyara asibitocin yankunan kananan hukumomin jihar 30 a karkashin kananan hukumomin jihar 27 duk a kokarin gwamnatin jihar na inganta harkokin kiwon Lafiya a fadin jihar

Kwamashina lafiya na Jihar Dr Abdullahi Kainuwa Hadejia shine ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa a ranar alhamis data gabata

Ya kara da cewar gwamnatin Kuma zata kafa injinan Sola da tirakun wutar lantarki na Sola tare da Samar da gidajen kwanan ma aikatan lafiya a daukacin asibitocin guda 30 da gwamnatin ta ware za ayiwa gyaran

Kuma za agina rijiyoyin burtsatse tareda hadasu da injin Sola domin Samarda ruwansha Mai tsafta a daukacin asibitocin da wanna aikin ya shafa

Ya kara da cewar gwamnatin ta ware naira miliyan 500 da zata dauki nauyin shirin social insurance domin marasa karfi wadda za arika tallafawa masu rashin lafiya da Mata masu juna da nakasassu da yara kanana a lokacin da basu da lafiya duk a karkashin kulawar wadancan asibitocin guda 30 da gwamnatin ta ware za ayi aikin .

Yace za a rika basu tallafin maganin ne kyauta Kamar yadda gwamnatin ta shirya ,saboda hakane ma gwamnatin jihar ta dauki kananan ma aikatan lafiya guda 867 da a kabasu cikakken aiki wato permanent

Haka zalika za a dauki manyan ma aikatan lafiya guda 200 da suka hada likitoci da masu bada maganguna da sauran manyan ma aikatan ungozoma yanzu haka an tantance mutane 180 wadanda za a rabasu a tsakanin wadancan asibitocin guda talatin da aka anbatasu a sama saboda mashinmancin Shirin da gwamnatin tasa agabanta

Yaci gaba da cewa gwamnati ta ware naira biliyan bakwai. Zata gina cibiyar gwaje gwaje a Dutse shedikwatar jihar Jigawa wadda a Cikin cibiyar za a samar da cat, lab wadda a nanne za a rika tiyatar zuciya da wanke Koda da lura da masu ciwon daji wato cancer ,Kuma za a Gina ita wanna cibiyar ne a Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa

Yakara da cewar Gwamnati zata Rika baiwa masu larurar ciwon Koda magani kyauta tareda sauya masu jini akan Kari ammafa zatayi hakane ga iyakacin Yan asalin jihar Jigawa kawai da nufin baiwa Al,umma kulawa akan Kiwon lafiyarsu

Yayinda gwamnatin jihar ta ware naira miliyan Dari biyar wadda za ayi anfani da it’a wajan Gina asibitin Kashi a karamar hukumar gumar Gumel a masarautar Gumel da nufin kulada lafiyar wadanda suke da Matsalar ciwon daya shafi kashi .

Daya juya batun ta adi da Iska tayi a makarantar Kiwon Lafiya dake jahun cewa yayi iskar tayi wa gwamnati shigar sauri Amma tuni aka warewa makarantar naira miliyan dari Tara da tamanin da daya wadda za a Samarda sabbin gine gine Masu kawatarwa domin makarantar ta amsa sunanta na kwaleji Kamar kowacce irin kwalejin Kiwon Lafiya ta Nigeria .

Yace suna Shirin Gina sabbin dakunan Daukar darasi da dakunan kwanan dalibai maza da Mata da yiwa makarantar kwalliya irinta zamani wato land scaping da Kuma Gina kofar makarantar wadda zatai daidai da mazani

Yace tuni suka duba matsalar da iskar ta haifar masu a makarantar harma an tura kwararru sun tantance abinda za a kashe Amma kananan aiyukan gyare gyare anriga an kammalasu karkashin kulawar shugaban makarantar dake jahun saboda dawowar dalibai wadda tuni sun rigaya sun Fara dawowa

Ya kara da cewar dukkan wadancan asibitocin 30 da gwamnati ta ware makudan kudade za a Yi masu gyaran ne a tsawon sati takwas Kuma a nasa ran kewayesu da katanga domin inganta tsaro da dukiya da lafiyar Al,ummar dake kwance a asibitin da Kuma ma aikatan da suke aiki a ciki

By ukarofi