Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Cibiyar Gargadin Ambaliya ta Ƙasa, FEWS, na Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Abuja, ta yi gargaɗin cewa an yi hasashen akwai wasu jihohi da za a samu ruwan sama mai yawa wanda zai iya haifar da ambaliya.
Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa mai yiwuwa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na tsawon kwanaki 4 daga ranar 21 zuwa 25 ga Yuni, 2024.
Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da; Jihar Adamawa: Abba Kumbo, Demsa, Farkumo, Ganye, Gbajili, Jimeta, Mubi, Natubi, Shelleng, Song, Wuro- Bokki, Mayo- Belwa; Jihar Benuwai: Agyo, Ugbokpo; Jihar Borno: Maiduguri; Jihar Jigawa: Hadejia; Jihar Kaduna: Kauru; Jihar Kano: Gezawa, Gwarzo, Kano, Karaye, Kunchi, Wudil; Jihar Katsina: Daura, Jibia.
Sauran Sun haɗa da; Jihar Kebbi: Argungun, Bagudo, Bunza, Gwandu, Ribah, Sakaba, Shanga, Yelwa; Jihar Kogi: Abejukolo, Omale, Zugbe, Jihar Nasarawa: Gidan Dogo, Keana, Lafia, Loko, Rukubi, Tunga, Udeni; Jihar Neja Niger; Magama; Jihar Filato: Langtang , Wase; Jihar Sokoto: Gagawa ,Goronyo, Isa, Shagari, Silame, Sokoto, Wamakko; Jihar Taraba: Bandawa, Donga, Kwata Kanawa, Lau, Ngaruwa, Yorro; da jihar Zamfara: Anka, Bukkuyum, Gummi.
Sakatare na dindindin, Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, Mahmud Kambari ya kuma yi kira a ranar Lahadin da ta gabata da a samar da amintaccen tsaftar muhalli da kayayyakin sarrafa shara a cikin yankunan a faɗin ƙasar, yana mai jaddada cewa hakan shi ne mabuɗin magance cututtuka masu yaɗuwa a ƙasar.
Ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da ranar tsaftar muhalli ta ƙasa a unguwar Piwoyi, Abuja, tare da taken “A kawar da shara, a zauna lafiya,” a ƙarshen mako.
Daraktan kula da gurbatar muhalli da kiwon lafiya na ma’aikatar muhalli Olubunmi Olusanya ne ya wakilce shi.
Ya ce, kayayyakin za su taimaka sosai wajen inganta lafiyar jama’a da kuma inganta yanayin tsaftar mutanen da ke barin yankunan karkara.
Ya yi kira ga al’umma da su riƙa tsaftace muhallinsu akai-akai domin daƙile yaɗuwar cututtuka kamar su kwalara, zazzaɓin typhoid da zazzaɓin Lassa.
Har ila yau, wakilin ƙungiyar Breakthrough Action Nigeria, wata ƙungiya mai zaman kanta, Jonathan Daku, ya ƙarfafa wa al’ummar karkara ƙwarin gwiwa da su kasance cikin halin tsafta, domin gurɓataccen muhalli yana haifar da cututtuka masu yaɗuwa.
Har ila yau, jami’in fasaha, Kiwon Lafiyar Jama’a da Muhalli, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dokta Edwin Edeh, ya yi alƙawarin tallafawa WHO ga gwamnati wajen bunƙasa atisayen a dukkan jihohi 36 na tarayya ciki har da Abuja.
Esu na Piwoyi, Cif Tanko Bayago, ya yaba wa ma’aikatar muhalli da abokan hulɗarta bisa zaɓar al’umma, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da wayar da kan al’umma kan tsaftar muhalli.
Muhimman abubuwan da suka faru a wannan atisayen sun haɗa da ziyarar fadar shugaban ƙasa, aikin tsaftace yankuna da kuma bada gudummawar kayayyakin tsaftace muhalli ga al’umma.
