
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya karɓi baƙoncin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan a fadar Sarkin da ke Gidan Rumfa, wanda haka ke nuna ƙarfin alaƙar da ke tsakaninsu.
Alaƙar tasu ta samo asali ne tun lokacin da Sarki Sanusi ke gwamnan babban bankin Nijeriya inda Dauda Lawan shi ne mai bashi shawara na musamman kan harkar bankin musulunci, wanda hakan ya taimaka wajen ƙirƙirar bankunan Ja’iz da TAJ da kuma Lotus gami da samar da tsare-tsare masu kyau a harkar banki.
Dauda Lawan, ya yi abin a yaba a harkar banki a Nijeriya inda a lokacin da ya riƙe muƙamin babban daraktan ɓangaren al’ummar Arewa a bankin ‘First Bank’, ya bada gudunmawa sosai a harkokin kuɗi, wanda hakan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya.
Ziyarar gwamnan ga Sarkin, zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakaninsu da kuma Masarautar Kano da jihar Zamfara, sannan hakan ya nuna kyakkyawar fahimtarsu da juna da kuma taya Sanusi murnar dawowa kan kujerar, biyo bayan tsige Mai Martaba Sarki Aminu Ado da gwamnatin Kano ta yi a watannin baya wanda ake cigaba da dambaruwa a kai.
