Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
Ina masu yin tadi ko zance a cikin mota tare da kunna ‘air conditioner’ da zuge gilashi? To, ku matso ku ji. Yin hakan yana da haɗari. Haɗarin shi ne idan iskar carbon monoxide da ya kamata ta tafi silencer ta samu kafa take shigowa cikin motarka. Mene ne illar hakan? Ku biyo ni.
A baya bayannan anan jihar Kano, an samu gawar wani mutum da wata mace a cikin mota sun mutu, sai da akayi dabaru wajen cire su daga motar saboda sun fara lalacewa. Abinda ya faru shi ne shi namijin ya kunna air conditioner alhalin motar tana kunne kuma ba tafiya take ba. Haka kuma gilasan motar a zuge suke yayin da suke tadin. To an samu akasi iskar carbon monoɗide ta yi ta shiga cikin motar alhalin shi mai motar da matar da suke taɗi ba su sani ba. Dalili kuwa shi ne ita wannan iska ba ta da wari bare ƙamshi, mutum zai shaƙeta bai ma sani a saboda babu wata alama da zai ji.
Idan iskar ta shiga jiki ta kafar numfashi, to za ta yi ta bi inda iskar oksijin take ta tunkuɗe ta, ta kuma maye gurbinta. Iskar carbon monoɗide guba ce a jiki. Idan mutum ya shaƙeta zuwa wani lokaci, za ta mamaye gaba ɗaya guraren da iskar oksijin ya kamata ta zauna, to daga nan kwayoyin halittar jiki sai su mutu tunda ba su samu iskar oksijin ba. Wannan shi ake kira da Carbon monoɗide Poisoning a turance.
Kamar yadda na faɗa iskar ba ta da wari ko ƙamshi. Saboda haka idan mutum ya na shaƙar ta babu wata alama da zai ji. Idan ta kai wani ƙadami a cikin jiki, mutum zai fara jin kansa yayi nauyi, zai fara jin bacci. To idan yayi bacci alhalin ya na ta shaƙar iskar, ƙwayoyin halittar jikinsa za su gaza saboda rashin oksijin, daga bisani shima sai yace ga garinku nan!
Saboda haka a kiyayi kunna AC alhalin an zuge gilas, koma mota a kunne, ba tafiya ta ke yi ba.
Fatan Allah Ya kiyaye. Amin
