Annobar Kwalara ta ɓarke a kurkukun Kirikiri, yayin da mutane 118 suka kamu a Katsina

Spread the love

Daga FAROUK ABBAS

Kwamishinan lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce sun samu rahoton mutane 25 da ake zargin suna ɗauke da cutar ƙwalara daga gidan yarin Kirikiri.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kula da gidajen yari (NCS) ta fitar da bayanin cewa babu mai ɗauke da cutar a gidan kurkukun a makon da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar ya ce sun ɗauki matakan kariya wajen ganin ba a samu ɓullar kwalara a gidan yarin ba.

Sai dai, ma’aikatar lafiya ta jihar Lagos ta offishin jami’in hulɗa da jama’a, Tunbosun Ogunbawo ta ce ta samu rahoton mutane 25 ɗin daga a Kirkiri.

A jihar Katsina kuma, cibiyar kula da cutuka da kare samuwar su ta ƙasa, ta ce ta samu rahoton zargi na mutum 118 da ke ɗauke da kwalara.

Cibiyar ta fitar da wani rahoto a ranar 24 ga watan Yuni, 2024 inda ta ce a ƙalla mutum 1,528 ne a ke zargi da cutar, yayinda aka tabbatar da 65 ɗauke da ita tare da mutuwar mutum 53, a ƙananan hukumomi 107 na Jihohi 31 a Nijeriya.

Jihohin da aka fi samun rahoton cutar sun haɗa da Bayelsa da Zamfara da Abia da Cross-River da Bauchi da Delta da Katsina da Imo da Nassarawa da kuma Lagas.

A ƙoƙarinta na magance yaɗuwar cutar, gwamnatin shugaba Tinubu ta ƙirƙiri kwamiti kan annobar ƙarƙashin ma’aikatar lafiya domin kula da lamarin a dukkan sassan Najeriya.

By Babaji