Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC, a ranar Lahadi ta ce kashi 100 na katin kira, SIM, da ake amfani da su a ƙasar ana yin su ne a cikin gida.
Babagana Digima, Shugaban Sabbin Kafafan Yaɗa Labarai da Tsaron Watsa Labarai na NCC ne ya bayyana haka a wurin horar da shugabannin kafafen yaɗa labarai a Legas.
Horon na kwanaki biyu yana da taken: “Haɓaka Ƙwararrun Masu Ruwa Da Tsaki Na Kafofin Watsa Labarai Akan Abubuwan Da Ke Faruwa A Harkar Sadarwa.”
Digima ya danganta hakan ne da jajircewar hukumar wajen ƙarfafa abubuwan cikin gida da kuma shiga cikin masana’antar ta ofishin cigaba na Nijeriya a sashin sadarwa na ‘Indigenous Telecommunications’ (NORDIT).
“Hukumar NCC ta sashe na 1D zuwa F na dokar mu ta bayyana aikinmu na ƙarfafa gwiwar ”yan asalin ƙasar da kamfanonin sadarwa da kuma manufofin ƙasa na inganta abubuwan da suka shafi ‘yan asalin yankin a ɓangaren sadarwa da suka kafa NORDIT.
“Haɗin gwiwar ‘yan asalin ƙasar na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da NORDIT ta taka rawar gani.
“A da, a cikin shekaru biyu da suka gabata, kusan kashi 99 cikin 100 zuwa kashi 100 na katin SIM ana shigo da su Nijeriya ne.
“Kuma lokacin da NORDIT ta zo, mun sanya shi ɗaya daga cikin manyan fifikonmu wadɗnda nan da watanni biyar zuwa watanni shida zai daina shigo da katin SIM.
“Mun umurci dukkanin kamfanonin sadarwa na Mobile Network Operators (MNOs) da su samar da katin SIM ɗinsu a cikin gida, kuma a gaskiya, a yanzu kashi 100 na duk katinan SIM da ake amfani da su a Nijeriya ana yin su ne a cikin gida, babu wanda ake shigo da shi daga waje,” inji Digima.
Digima, tsohon shugaban NORDIT, ya bayyana cewa hukumar ta NORDIT ta tsunduma cikin ayyukan bayar da shawarwari don ƙarfafa gwiwar ‘yan asalin gida na kamfanoni da jama’a a kowane ɓangare na sadarwa.
Ya ce NORDIT ta kuma bayar da tallafi ga wasu kamfanoni don tabbatar da cigaban masana’antar.
“A yanzu haka, muna ɗaukar nauyin ƙera Corrugated Ordinal Duct, kuma kamfanin da za a kafa shi ne na farko a duk faɗin Afirka wajen ƙera irin wannan nau’in na’ura,” inji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, mataimakin shugaban hukumar NCC, Dr Aminu Maida, ya ce an ɗauki wannan shiri na ƙara wa manyan jami’an yaɗa labarai ƙwarewa ne saboda buƙatar cike giɓin da ke tsakanin hukumar da yadda jama’a suka fahimci hakan.
