Bulalar malamar makaranta ta yi sanadiyyar mutuwar wani ɗalibi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukuma ta tsare wata malamar makaranta a jihar Anambara sakamakon mutuwar wani ɗalibinta ɗan kimanin shekara 8.

Malamar mai suna Faith Nwoye, ta kasance mai koyarwa ce a Landmark International School da ke Mbakwu a ƙaramar hukumar Akwa ta Arewa a jihar, wacce ta zane Henry Okonkwo da bulala wanda daga bisani ya mutu.

Ganin haka ke da wuya, sai a ka shigar da ita ƙara a wata kotu da ke aiki kan lumuran da suka shafi mata da yara inda a nan a ka yanke hukuncin tsare ta a gidan gyaran hali.

An shigar da shugaban makarantar, Promise Iloh da malamar ƙara kan lalamrin ne bayan da wani Ojiakor Okonkwo ya rubuta takardar neman bincike kan musabbabin mutuwar yaron ga kwamishinar ma’aikatar ilmi ta jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Ude inda aka gayyace su domin yin bayanin abin da ya halaka yaron, wanda daga baya kotun ta miƙa lamarin ga hukumar ‘Yan sanda domin cigaba da bincike.

Farfesa Ngozi ta bada umarnin a gaggauta rufe makarantar ganin yadda a ke samun ƙorafe-ƙorafe kan yanayin gudanarwarta.

Ngozi ta ƙara da cewa, matuƙar ‘Yan sandan su ka kammala bincike kuma su ka tabbatar da laifin a kan malamar, to doka za ta yi aiki a kanta.

Kazalika, an samu kiraye-kiraye daga al’ummar da hukumomin jihar da a ƙara sanya ido kan gudanar makarantu tare da samar da hanyoyin kare aukuwar irin haka a nan gaba.

By Babaji