Ɗan Majalisar Wakilai daga Abiya ya nemi Buhari ya sa baki kan sakin Kanu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan majalisa Obi Aguocha (jami’iyyar LP a Abia) ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tare da buƙatar sa baki don ganin an sako Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara, IPOB.

Aguocha, mai wakiltar mazaɓar Ikwuano/Umuahia ta Arewa/Umuahia ta kudu a jihar Abia, ya bayyana ma’anar ziyarar ta sa a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce, ya je Katsina ne domin ya nemi Buhari ya shiga tsakani da kuma neman goyon bayan sa don tattaunawa ta siyasa da kuma kyakkyawar alaƙa.

Wannan, a cewarsa, zai haifar da warware muhimman batutuwan da suka shafi ci gaba da tsare Kanu da kuma shari’a, “wanda zai iya kai ga sake shi bisa la’akari da matakan sulhu na ƙasa”.

Ya ce, “saboda kuskure, kalamai da munanan kalamai da aka yi a baya, musamman ta ɓangaren mazaɓa kuma ɗan uwana, Nnamdi Kanu, na yi matuƙar nadama.”

Aguocha ya kuma bayyana imaninsa cewa ƙudurin siyasa ba wai kawai zai magance ƙorafe-ƙorafen jam’iyyu daga kowane ɓangare ba, har ma da ƙara fahimtar juna da haɗin kai a aasar.

Sanarwar ta ruwaito Buhari na yaba wa tsayuwa da jajircewar ɗan majalisar wajen yi wa al’ummarsa hidima.

An kuma ambato Buhari ya tabbatar wa ɗan majalisar cewa an yi marhabin da matakin da ya ɗauka, kuma ba zai yi adawa da duk wata mafita ta siyasa don a sako Kanu ba.

Idan za a iya tunawa, kwanan nan Aguocha ya jagoranci gungun ‘yan majalisar wakilai 50 a faɗin ɓangaran siyasa da ƙabilanci inda suka rattaba hannu kan wata wasiƙa da ke kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya saki Kanu.

Wasikar ta buƙaci Tinubu ya umurci babban Lauyan ƙasar kuma ministan shari’a, Lateef Fegbemi (SAN) “da ya yi amfani da sashe na 174(1) (c) na kundin tsarin mulkin 1999 domin cimma matsaya da ake buƙata”.

Ɗan majalisar ya cigaba da cewa ganawar da Buhari na daga cikin manyan tsare-tsare da nufin ganin an gaggauta magance matsalar tsare Kanu da kuma shari’a a siyasance.

By ukarofi